HALITTARSA AKA YI?
Abu Mai Yauki da Ke Jikin Kifin da Ake Kira Hagfish
’Yan kimiyya sun dade suna mamakin wani abu mai yauki da ke fitowa daga jikin hagfish. Me ya sa yake burge su? Sun ce yana cikin “abubuwa da ake iya ja kamar roba, kuma yana cikin abubuwa mafi laushi da aka taba gani.”
Ka yi tunani a kan wannan: Hagfish wani irin kifi ne da ke kama da maciji kuma yana zama a karkashin teku. Idan wata halitta ta zo ta cinye shi, yakan fitar da wani abu mai yauki daga wasu ramuka da ke jikinsa. Wannan abin da yake fitarwa yana dauke da dubban sinadaran furotin dabam-dabam. Wasu sinadaran suna da yauki, wasu kuma zare-zare suke. Wadannan sinadaran furotin sukan garwayu da ruwan da ke kewaye da kifin sai su dawo kamar gam mai yauki. Wannan abu mai yaukin ne yake shake duk wata halitta da ke kokarin cinye kifin, kuma ya sa ta tufar da shi nan da nan ta gudu.
Wannan abu mai yauki da ke fitowa daga jikin hagfish bai da na biyunsa. Irin sinadaran furotin da ke cikinsa suna kama da kananan zare. Zare-zaren nan ’yan mitsitsi ne, wanda sai an raba kaurin gashin mutum sau dari kafin a sami daya. Amma ya fi zaren nylon da ake yin yadi da shi karfi har sau goma. Idan kifin ya zuba sinadaran nan a ruwan teku, sai yauki-yaukin da zare-zaren su zama kamar raga mai laushi. Wannan ragar za ta iya rike ruwa da ya fi ta nauyi sau 26,000. Yana kamar ruwa ne zalla!
’Yan kimiyya sun kasa kirkiro irin abu mai yauki da hagfish yake fitarwa. Wani mai yin bincike ya ce: “Wannan abin na da wuyar fahimta sosai.” Duk da haka, ’yan kimiyya suna so su samar da irin sinadaran furotin da kifin yake fitarwa ta wajen amfani da kwayoyin halitta da ake kira bacteria. Nufinsu shi ne su samo abin da bai da nauyi, da ba ya yagewa da wuri, da ake iya ja kamar roba, kuma abubuwa kamar bacteria za su iya narkar da shi. Idan an iya samar da irin zare-zaren furotin da kifin yake fitarwa, za a iya amfani da su wajen yin yadi da wasu kayan amfanin likitoci, kuma za a iya ci gaba da samunsu a saukake. Hakika, za a iya amfani da wannan abin a hanyoyi da yawa.
Mene ne ra’ayinka? Kana ganin cewa yadda aka tsara wannan abu mai yauki da ke fitowa daga jikin hagfish sakamakon juyin halitta ne? Ko akwai wanda ya halicce shi?