HALITTARSA AKA YI?
Harshen Kule
An san kule da tsabtace jikinsa. Idan ba barci kule yake yi ba, zai iya daukan wajen awa daya cikin awa hudu yana gyara gashinsa. Yadda aka tsara harshensu ne ya sa suke iya tsabtace jikinsu haka.
Ka yi tunani a kan wannan: Kule yana da wasu kananan abubuwa guda 290 da suke jikin harshensa. Wadannan abubuwan suna da tsini kuma suna da tauri kamar farshe. Sa’an nan an jera su yadda za su fuskanci cikin bakinsa. Kowannensu yana da rami da ke diban yawu a duk lokacin da kulen ya mai da harshen cikin bakinsa. Yayin da kulen yake lashe gashinsa, abubuwan nan sukan bi cikin gashinsa kuma su shafa yawun a fatarsa.
Kule zai iya amfani da harshensa ya shafa wa fatarsa yawu wajen cokali uku kowace rana. Yawun yana dauke da sinadaran da ke narkar da datti da ke jikin kulen. Kari ga haka, yayin da iska take busar da yawun, yana taimakawa wajen rage wa kulen zafin jikinsa. Hakan na da muhimmanci sosai don kule ba ya zufa sosai.
Idan daya daga cikin abubuwan nan ya gamu da gashin da ya nannadu, yakan shiga cikin gashin kuma ya tsefe su. Kari ga haka, tsininsa yakan sosa fatar kulen kuma ya inganta ta. Masu bincike sun kera wani abin tsefe gashi da ke da tsari irin na abubuwan da ke harshen kule. Wannan abin tsefe gashi yana da sauki a yi amfani da shi fiye da wadanda aka saba amfani da su. Tsabtace shi bai da wuya kuma yana warware gashi da kyau. Masu binciken sun kuma tabbata cewa bin tsarin harshen kule zai taimaka musu wajen samar da ingantattun hanyoyin tsabtace abubuwa da jikinsu yake da gashi-gashi. Za a kuma iya amfani da shi wajen inganta yadda ake shafa mai ko magunguna a gabobin jiki da gashi ya rufe su.
Mene ne ra’ayinka? Kana ganin yadda aka tsara harshen kule sakamakon juyin halitta ne? Ko akwai wanda ya halicce shi?