Koma ka ga abin da ke ciki

KA YI KOYI DA BANGASKIYARSU | AYUBA

Jehobah Ya Warkar da Shi

Jehobah Ya Warkar da Shi

A karshe, sai kowa ya yi shiru. Watakila abin da kawai ake ji shi ne karar iska mai dumi da take hurowa daga hamadar Larabawa. Ayuba ya rasa abin da zai fada, ya gaji sosai bayan doguwar mahawara. Ka yi tunanin yadda yake hararar aminansa guda uku ransa a bace, kamar yana ce musu su ci gaba mana. Sunayensu Elifaz da Bildad da Zofar. Ba su iya daga ido su kalle shi ba, domin duk mahawararsu da maganganun banza da suka yi game da Ayuba bai yi tasiri ba. (Ayuba 16:3) Abin da ya fi damun Ayuba shi ne yadda zai tabbatar musu cewa shi mai aminci ne.

Watakila abin da ya rage wa Ayuba da yake gadara da shi, shi ne amincinsa. Ya yi hasarar dukiyarsa da ’ya’yansa goma, kuma abokansa da makwabtansa sun daina kula shi da daraja shi. Kari ga haka, ya soma rashin lafiya. Fatar jikinsa ta yi baki saboda cutar, ga kuraje ko’ina a jikinsa har tsutsa suna fitowa. Numfashinsa ma yana wari. (Ayuba 7:5; 19:17; 30:30) Har ila, maganganu marasa dadi da abokansa guda uku suka gaya masa ya sa shi fushi sosai. Don haka, ya dage wajen nuna musu cewa shi ba mugu ba ne kamar yadda suka fada. Maganar Ayuba ta karshe ta sa sun rasa abin da za su fada. Sun rasa bakar maganar da za su sake gaya masa. Amma bakin cikin Ayuba bai kare ba. Kuma yana bukatar taimako ruwa a jallo.

Tunanin Ayuba bai dace ba kuma bai kamata mu ga laifinsa ba domin yana bukatar ja-goranci da gyara. Yana bukatar karfafa da kuma ta’aziyya, abin da ya kamata abokansa uku su yi masa ke nan, amma ba su yi hakan ba. Ka taba shiga yanayi mai wuya da ka bukaci a ba ka shawara kuma a karfafa ka? Wadanda kake ganin abokanka ne sun taba juya maka baya? Koyan yadda Jehobah Allah ya taimaki bawansa Ayuba da kuma yadda Ayuba ya amince da taimakon, zai iya ba ka bege ya kuma taimaka maka.

Mashawarci Mai Alheri da Hikima

Ana nan ana nan, sai ga wani abin da ba mu yi zato ba. Akwai wani mutum da ke wurin da bai kai su shekaru ba, sunansa Elihu. Yana wurin tuntuni, ya yi shiru yana jin mahawarar da dattiban suke yi. Abin da ya ji ya bata masa rai.

Elihu ya yi fushi da Ayuba. Ransa ya bace don yadda Ayuba ya bar maganganun da abokansa suka fada ya sa “ya nace a kan adalcinsa fiye da adalcin Allah.” Duk da haka, Elihu ya ji tausayin Ayuba, don ya lura da zafin da Ayuba yake ji. Kari ga haka, ya ga cewa shi ba mugu ba ne kuma yana bukatar shawarar kirki da ta’aziyya sosai. Shi ya sa Elihu bai ji dadin abin da abokan Ayuba guda uku suka yi ba. Ya ji yadda suke gaya wa Ayuba bakar magana, suna kokarin nuna cewa ba shi da bangaskiya da mutunci da kuma aminci. Abin da ya fi muni shi ne, maganganun da suka yi ya nuna kamar Allah mugu ne. Abubuwan nan sun sa Elihu ya ga cewa ya kamata ya yi magana.​—Ayuba 32:​2-4, 18.

Elihu ya ce: “A shekaru dai ni yaro ne, ku tsofaffi ne a gare ni. Wannan ya sa na ji nauyi na kuma ji tsoro in fada muku abin da na sani.” Amma bai ci gaba da yin shiru ba. Ya dada da cewa: “Ba wai zama tsoho ne yakan kawo hikima ba, ba kuma yawan shekaru ne yakan kawo ganewar yin shari’ar gaskiya ba.” (Ayuba 32:​6, 9) Sai Elihu ya yi magana sosai don ya tabbatar da cewa abin da ya fada gaskiya ne. Ra’ayinsa ba daya ba ne da na Elifaz da Bildad da Zofar. Elihu ya tabbatar wa Ayuba cewa ba zai yi masa maganar reni ko ya kara masa damuwa ba. Amma ya girmama Ayuba ta kiran sa da sunansa kuma ya yarda cewa an wulakanta Ayuba. * Cikin ladabi, ya ce: “Amma yanzu ya Ayuba, Ina rokonka, ka ji dukan kalmomina.”​—Ayuba 33:​1, 7; 34:7.

Elihu ya kira Ayuba da sunansa, ya yi masa maganar alheri kuma ya daraja shi

Elihu ya gaya wa Ayuba gaskiya, ya ce: “Hakika, abin da ka fada, na ji da kunnena . . . Ka ce, ‘ni mai tsabtar zuciya ne, ba ni da zunubi, ina da tsabtar rai, ba ni da laifi. Ga shi, Allah yana neman dalili a kaina.’” Elihu ya bayyana ainihin inda damuwar take, ta wurin yi masa tambaya cewa: “Daidai ne wannan a ganinka? Adalcina ya fi na Allah, in ji ka.” Elihu bai kyale Ayuba ya ci gaba da wannan tunanin ba. Ya ce masa, “Ba ka da gaskiya.” (Ayuba 33:​8-12; 35:​2, Tsohuwar Hausa a Saukake) Elihu ya san Ayuba yana fushi sosai saboda hasarar da ya yi, da kuma wulakancin da ya sha daga wurin abokansa marasa kirki. Amma Elihu ya gargadi Ayuba ya ce: “Ka lura fa, kada ka sa kanka ga yin mugunta.”​—Ayuba 36:21.

Elihu Ya Bayyana Alherin Jehobah

Abu mafi muhimmanci shi ne, yadda Elihu ya kāre sunan Jehobah. Ya bayyana wata gaskiya mai muhimmanci sa’ad da ya ce, “Allah ba zai taba aikata mugunta ba! A wurin Mai Iko Duka babu kuskure! . . . Mai Iko Duka ba zai jujjuye gaskiya ba.” (Ayuba 34:​10, 12) Elihu ya taimaka wa Ayuba ya ga cewa Jehobah Allah ne mai jinkai da adalci. Domin ko da yake Ayuba ya fi mai da hankali ga kansa kuma ya yi wa Allah maganganun reni, Allah bai yi masa horo ba. (Ayuba 35:​13-15) Elihu bai nuna cewa ya san kome game da Allah ba, maimakon haka ya nuna saukin kai, ya ce: “Hakika Allah da girma yake sosai! Ba mu kuwa san iyakar daukakarsa ba.”​—Ayuba 36:26.

Ko da yake shawararsa gaskiya ce, Elihu ya yi masa maganar alheri. Ya yi maganar da ta nuna cewa, wata rana Jehobah zai warkar da Ayuba, wannan bege ne mai kyau sosai. Ya annabta cewa: “Jikinsa zai sabunta fiye da na saurayi, zai komo kamar na kwanakin kuruciyarsa.” Wani abin alheri kuma da Elihu ya yi shi ne, maimakon shi kadai ya ta jawabi, ya ba wa Ayuba dama ya yi magana. Ya ce: “Ka amsa mini, . . . gama ina so in nuna a fili cewa ba ka da laifi.” (Ayuba 33:​25, 32) Amma Ayuba bai amsa ba. Watakila Ayuba ya yi shiru ne domin kalaman Elihu sun karfafa shi sosai kuma ya ga cewa ba ya bukatar ba da wata hujja. Mai yiwuwa ya yi kuka saboda karfafar da ya samu.

Za mu iya koyan abubuwa masu yawa daga wurin Elihu da Ayuba. Daga wurin Elihu, mun koyi yadda ya kamata mu shawarci da kuma karfafa wadanda suke cikin damuwa. Aboki na kwarai ba zai ki nuna wa abokinsa inda ya yi laifi ko ya ja masa kunne in yana so ya yi wani abin da bai dace ba. (Karin Magana 27:6) Muna so mu zama kamar wannan abokin, mu nuna wa mutane alheri kuma mu karfafa su, ko da halin da suke ciki ya sa sun fadi abin da bai dace ba. Kuma idan mu ne aka yi wa gyara, zai dace mu nuna saukin kai kuma mu karbi gyarar kamar yadda Ayuba ya yi, maimakon mu yi watsi da ita. Dukanmu na bukatar shawara da gyara. Yin na’am da su zai ceci rayukanmu.​—Karin Magana 4:13.

“Daga Cikin Guguwa”

Sa’ad da Elihu yake magana, sau da yawa ya ambata iska, gajimare, tsawa da walkiya. Ya yi magana game da Jehobah, ya ce: “Kasa kunne ku ji karar muryarsa.” Jim kadan bayan haka, Elihu ya yi magana game da “guguwa.” (Ayuba 37:​2, 9) Mai yiwuwa da yake magana, sun ga guguwa tana tasowa, tana dada karfi. A karshe, ta zama guguwa mai karfin gaske. Sai wani abin ban mamaki ya faru. Jehobah ya fara magana!​—Ayuba 38:1.

Da a ce kana wurin sa’ad da Mahaliccin sama da kasa yake yin bayani a kan halittun nan, da ya za ka ji?

Mukan yi farin ciki a duk lokacin da muke karanta littafin Ayuba kuma muka kai inda Jehobah ya yi magana da Ayuba. Kamar yadda guguwa take hura datti ta tafi da shi, haka ma abubuwan da Jehobah ya fada suka kawar da maganganun banza da Elifaz da Bildad da Zofar suka yi. Jehobah bai ma yi magana da su ukun ba sai daga baya. Ya mai da hankali ga Ayuba ne kadai, kuma kamar yadda uba zai yi wa dansa gyara cikin kauna, haka ya yi wa Ayuba bawansa.

Jehobah ya san azabar da Ayuba yake sha kuma ya ji tausayin sa, kamar yadda yake yi idan ya ga ’ya’yansa da yake kauna suna shan wahala. (Ishaya 63:9; Zakariya 2:8) Amma ya san cewa, Ayuba ya yi “maganganun jahilci,” kuma hakan ya dada bata lamarin. Don haka, Jehobah ya fahimtar da Ayuba ta wajen yi masa tambayoyi masu yawa. Ya fara da cewa: “Ina kake lokacin da na kafa tushen duniya? Fada mini idan ka gane.” A farkon halitta, “taurarin safiya,” wato mala’iku, sun tā da muryar farin ciki saboda abin ban mamaki da suka gani. (Ayuba 38:​2, 4, 7) Ayuba ya kasa ba da amsa don bai san kome game da wannan ba.

Jehobah ya yi magana daga cikin guguwa kuma cikin kauna ya daidaita tunanin Ayuba

Jehobah ya ci gaba da magana a kan halittunsa. Za mu iya cewa Jehobah ya yi wa Ayuba bayani a kan batutuwa kamar ilimin taurari, ilimin halitta, ilimin kasa da kuma ilimin kimiyyar lissafi wato physics. Jehobah ya yi bayani musamman a kan wasu dabbobi da ke yankin da Ayuba yake zama, irin su, zaki da hankaka da awakin dutse da jakin daji, bijimin daji, jimina, doki, shaho, gaggafa, Behemot (watakila dorinar ruwa) da kuma Lebiyatan (mai yiwuwa kada). Da a ce kana wurin sa’ad da Mahaliccin sama da kasa yake yin bayani a kan halittun nan, da ya za ka ji? *

Darasi a kan Saukin Kai da Kauna

Mene ne Allah yake so ya koya wa Ayuba? Ayuba yana bukata ya dada zama mai saukin kai. Ayuba ya yi gunaguni domin yana ganin Allah ne yake wulakanci shi. Amma yin hakan ya sa Ayuba ya kara wa kansa azaba, kuma ya nisanta kansa daga Ubansa mai kauna. Jehobah ya tambayi Ayuba sau da yawa cewa ina yake lokacin da ya halicci abubuwan nan masu ban al’ajabi, kuma ko zai iya ciyar da su, ya kula su, ko ya ja-gorance su. Idan Ayuba ba zai iya yin hakan ba, yaya yake ganin zai iya gaya wa Mahalicci abin da ya kamata ya yi? Jehobah ya san abin da ya kamata a yi da yadda za a yi hakan, kuma Ayuba ba zai iya fahimtar hakan kamar Jehobah ba.

Ayuba bai yi mūsu da Jehobah ko ya ba da hujja ba

Dukan abubuwan da Jehobah ya fada sun nuna cewa yana kaunar Ayuba sosai. Kamar dai Jehobah yana taimaka wa Ayuba ya yi tunani ne, yana cewa: ‘Dana, idan zan iya halitta da kuma kula da wadannan abubuwan, kana ganin zan kasa kula da kai? Kana ganin zan juya maka baya, in kashe ’ya’yanka, in sa ka rashin lafiya kuma in hana ka sakewa? Ba ni kadai ne zan iya mayar maka da abubuwan da ka yi hasararsu kuma in kawar maka da azabarka ba?’

Sau biyu kawai Ayuba ya amsa tambayoyin da Jehobah ya yi masa. Bai yi mūsu ko ya ba da hujja ba. A cikin saukin kai ya yarda cewa abin da ya sani kadan ne, kuma ya tuba don kalaman da ya fada da garaje. (Ayuba 40:​4, 5; 42:​1-6) Nan ya nuna mana irin bangaskiyar da Ayuba yake da shi. Duk da matsalolin da ya fuskanta, bai daina kasancewa da bangaskiya ba. Ya yi na’am da gyarar da Jehobah ya yi masa kuma ya canja ra’ayinsa. Wannan zai iya sa mu tambayi kanmu, ‘Ina karban gyara da horo a cikin saukin kai kuwa?’ Hakan zai amfane mu sosai. Idan muka karbi gyara, muna yin koyi da bangaskiyar Ayuba.

“Ba Ku Fadi Gaskiya Game da Ni” Ba

Jehobah ya dauki mataki don ya ta’azantar da Ayuba. Da Jehobah yake magana da Elifaz, wanda kamar shi ne babba a cikin maza ukun, ya ce: “Fushina ya kunnu a kanka da abokan nan naka biyu, gama ba ku fada gaskiya game da ni kamar yadda bawana Ayuba ya yi ba.” (Ayuba 42:7) Ka yi tunanin wadannan kalaman. Shin Jehobah yana nufin cewa dukan kalaman da maza ukun nan suka yi karya ne ko kuma dukan kalaman da Ayuba ya furta gaskiya ne? A’a. * Amma yanayin Ayuba ba daya ba ne da na masu tuhumarsa. Ayuba yana cikin bakin ciki don irin wahalar da yake fuskanta da kuma karyar da aka yi masa. Babu shakka, wadannan abubuwan ne suka sa ya yi magana da garaje a wasu lokuta. Amma Elifaz da abokansa biyu ba abin da ya same su. Da gangan suka yi wa Ayuba bakar magana domin su masu girman kai ne kuma ba su da bangaskiya. Sun wulakanta mutum marar laifi, kuma sun yi maganganun da suka nuna kamar Jehobah mugu ne marar tausayi.

Shi ya sa Jehobah ya gaya wa mazan nan cewa su yi hadaya mai tsada don neman gafara. Ya gaya musu su yi hadaya da bijimai bakwai da raguna bakwai. Hakan ba karamar hadaya ba ce domin daga baya, a cikin Dokar da aka bayar ta hannun Musa, an bukaci babban firist ya ba da hadayar bijimi idan zunubin da ya yi ya shafi dukan al’ummar Isra’ila. (Littafin Firistoci 4:3) Bijimi ne dabba mafi tsada da ake hadaya da ita a karkashin Dokar. Kari ga haka, Jehobah ya ce ba zai karbi hadayar masu tuhumar Ayuba ba sai Ayuba ya yi addu’a a madadinsu. * (Ayuba 42:8) Babu shakka, Ayuba ya ji dadi sa’ad da Allahnsa ya wanke shi daga zargin da ake masa kuma Jehobah ya nuna cewa shi mai adalci ne.

“Bawana Ayuba zai yi addu’a domin ku.”​—Ayuba 42:8

Jehobah ya tabbata cewa Ayuba zai yi abin da ya umarce shi ya yi, zai gafarci mazan nan da suka sa shi bakin ciki sosai. Kuma Ayuba bai kunyatar da Ubansa ba. (Ayuba 42:9) Ko da yake kalaman Ayuba sun nuna cewa shi mai aminci ne, amma ayyukansa ne suka fi nuna hakan. Kuma abin da ya sa Jehobah ya yi masa albarka sosai ke nan.

“Mai Jinkai Ne”

Jehobah ya nuna wa Ayuba cewa shi “mai jinkai ne, mai yawan tausayi kuma.” (Yakub 5:11) Ta yaya? Jehobah ya warkar da Ayuba. Ka yi tunanin yadda Ayuba ya ji sa’ad da ya ga cewa jikinsa ya “sabunta fiye da na saurayi,” kamar yadda Elihu ya annabta! A karshe danginsa da abokansa sun zo wurinsa, sun karfafa shi kuma sun ba shi kyaututtuka da yawa. Jehobah ya sa Ayuba ya sami ninki biyu na abin da yake da shi a dā. Mene ne Jehobah ya yi game da mutuwar ’ya’yan Ayuba, wadda ita ce ta fi sa shi bakin ciki? Ayuba da matarsa sun kara haifan ’ya’ya goma! Babu shakka, hakan ya ta’azantar da su. Ban da haka, Jehobah ya kara masa shekaru. Allah ya kara masa shekaru 140, kuma ya ga yaransa da ’ya’yan yaransa har tsara ta hudu. A karshe, Littafi Mai Tsarki ya ce, “Ayuba kuwa ya mutu cikin tsufa sosai.” (Ayuba 42:​10-17) Kuma a cikin Aljanna, Ayuba da matarsa za su sake haduwa da danginsu har da ’ya’yansu goma da Shaidan ya kashe.​—Yohanna 5:​28, 29.

Me ya sa Jehobah ya ba Ayuba lada da yawa haka? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kun dai ji irin jimrewar da Ayuba ya yi.” (Yakub 5:11) Ayuba ya jimre tsanani fiye da yadda muke tsammani. Kalmar nan “jimrewa” ta nuna cewa ba hakuri kawai Ayuba ya yi da matsalolinsa ba, amma ya ci gaba da kasancewa da bangaskiya, kuma bai daina kaunar Jehobah ba. Maimakon ya yi fushi ko ya rama abin da aka yi masa, ya gafarta ma wadanda suka wulakanta shi har da maza ukun da suka sa shi bakin ciki da gangan. Bai yi watsi da begensa da kuma amincinsa ba.​—Ayuba 27:5.

Kowannenmu yana bukatar ya jimre. Ba shakka, Shaidan zai yi kokari ya sa mu sanyin gwiwa kamar yadda ya yi wa Ayuba. Amma idan muka jimre, muka ci gaba da zama da saukin kai, muka gafarta wa mutane, kuma muka rike amincinmu, za mu sa rai cewa abubuwa za su gyaru a nan gaba. (Ibraniyawa 10:36) Idan muka yi koyi da bangaskiyar Ayuba, hakan zai sa Shaidan bakin ciki kuma ya faranta wa Jehobah rai.

^ sakin layi na 6 Maganganun da Elifaz, Bildad da Zofar suka yi wa Ayuba za su iya cika surori tara na Littafi Mai Tsarki, amma ko sau daya ba su kira Ayuba da sunansa ba.

^ sakin layi na 14 A wasu lokuta, Jehobah ya yi magana a kan batutuwan nan a zahiri, a wasu lokuta kuma ya yi amfani da kwatanci. (Ka ga wasu misalai a Ayuba 41:​1, 7, 8, 19-21.) Allah ya yi hakan ne domin ya taimaki Ayuba ya kara girmama Mahaliccinsa.

^ sakin layi na 18 Akwai lokacin da manzo Bulus ya yi kaulin wani furucin da Elifaz ya yi kuma ya nuna cewa furucin gaskiya ne. (Ayuba 5:13; 1 Korintiyawa 3:19) Abin da Elifaz ya fada gaskiya ne amma ba Ayuba ya kamata ya gaya wa hakan ba.

^ sakin layi na 19 Ba wurin da ya nuna cewa an bukaci Ayuba ya mika hadaya a madadin matarsa.