TAIMAKO DON IYALI
Yadda Za Ka Kame Kanka Idan Ka Yi Fushi
Mijinki ko matarka ta yi abin da ya bata maka rai, amma ka yi kokarin boye bacin ranka. Sai matarka ta gano cewa da akwai abin da ke damunka kuma ta soma tambayar ka. Hakan ya dada bata maka rai. Ta yaya za ka kame kanka a irin wannan yanayin?
Abin da ya kamata ka sani
Yin fushi yana iya cutar da kai. Masu bincike sun gano cewa idan mutum yana yawan yin fushi hakan yana iya jawo hawan jini ko ciwon zuciya ko yawan bakin ciki ko kuma ciwon ciki. Kari ga haka, yawan fushi yana iya sa rashin barci da alhini da cuta a fatar jiki da kuma bugun jini. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce “Kada ka yi fushi, wannan ba ya kawo kome sai mugunta.”—Zabura 37:8.
Boye bacin rai yana iya yi maka lahani. Idan ka ci gaba da yin fushi, hakan yana iya zama kamar wata cuta da ke jawo maka lahani a cikin jiki. Alal misali, kana iya zama mai yawan kushe mutane. Zama da mutum mai irin wannan halin yana da wuya sosai kuma zai iya jawo matsala a aurenka.
Abin da za ka iya yi
Ki mai da hankali ga halaye masu kyau na mijinki ko matarka. Ki lissafa halaye uku masu kyau na mijinki ko matarka da kake so. Idan mijinki ko matarka ta yi abin da ya bata maka rai ka tuna da halayenta uku da kake so da ka lissafa. Yin hakan yana iya taimaka maka ka kame kanka kuma ka guji yin fushi.
Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Ku kuma kasance masu godiya.”—Kolosiyawa 3:15.
Ka zama mai gafartawa. Da farko, ka yi kokarin fahimtar matarka ko mijinki. Yin hakan zai taimaka maka ka soma nuna tausayi. (1 Bitrus 3:8) Bayan haka, ka tambayi kanka ‘Abin da aka yi mini yana da muni sosai ne da ba zan iya gafartawa ba?’
Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Kyale laifin da aka yi . . . abu ne mai kawo . . . daraja.”—Karin Magana 19:11.
Ka fadi abin da ke zuciyarka a hanyar da ta dace kuma da basira. Ka yi amfani da kalmar nan “Ni.” Alal misali, maimakon ki ce, “A ganina ba ka damu da ni ba, domin ba ka kira ka gaya mini wurin da kake,” zai fi dacewa ki ce, “Ina damuwa sosai idan dare ya yi kuma ban san ko lafiyar ka ba.” Fadin abin da ke zuciyarka a cikin kwanciyar hankali zai iya sa ka kame kanka.
Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “A koyaushe, bari maganarku ta kasance da alheri da kuma dadin ji.”—Kolosiyawa 4:6.
Ka saurara da kyau. Bayan ka fadi abin da ke zuciyarka, ka bar matarka ko mijinki ya yi magana ba tare da katse masa magana ba. Bayan haka, ki maimaita abin da ya fada don ki tabbatar kin fahimce shi da kyau. Saurara da kyau zai iya taimaka maka ka kame kanka.
Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Kowa ya kasance mai saurin ji, amma ba mai saurin magana ba.”—Yakub 1:19.