Koma ka ga abin da ke ciki

Iyayena Ba Sa Kyale Ni Na Yi Nishadi

Iyayena Ba Sa Kyale Ni Na Yi Nishadi

Ka la’akari da yanayin da ke gaba:

Kana son ka fita liyafa, amma ba ka san ko iyayenka za su yarda ba. Wane mataki za dauka?

  1.  KADA KA NEMI IZINI, KA TAFI KAWAI

  2.  KADA KA NEMI IZINI, KUMA KADA KA TAFI

  3.  KA NEMI IZINI, KUMA KA SAURARA

 1. KADA KA NEMI IZINI, KA TAFI KAWAI

 Ga abin da ya sa kila ka dauki wannan matakin: Kana son ka nuna wa abokanka cewa kana da ’yancin kanka. Kana jin cewa ka fi iyayenka sani, ko kuma ba ka daraja shawararsu.—Misalai 14:18.

 Sakamakon: Kana iya burge abokanka, amma za su san ka da wani abu—cewa kai dan rudu ne. Idan ka rudi iyayenka, za ka iya rudin abokanka ma. Idan iyayenka suka sani, za su yi bakin ciki kuma ka san cewa ka ci amanarsu, kuma kila a yi maka horo!—Misalai 12:15.

 2. KADA KA NEMI IZINI, KUMA KADA KA TAFI

 Ga abin da ya sa kila ka dauki wannan matakin: Ka yi tunaninsa kuma ka ga cewa abin da za a yi a wajen zai rage mutuncinka ko kuma wasu da aka gayyata ba mutanen kirki ba ne. (1 Korintiyawa15:33; Filibiyawa 4:8) A wani sashe kuma, kana so ka je amma kana tsoron gaya wa iyayenka.

 Sakamakon: Idan ka ki tafiya don ka san bai dace ba, za ka kasance da gaba gadi yayin da kake bayyana wa abokanka ba. Amma idan ka ki tafiya domin kana tsoron ka gaya wa iyayenka ne, to za ka zauna a gida zugum, kana ganin kai kadai ne ba ka nishadi.

 3. KA NEMI IZINI, KUMA KA SAURARA

 Ga abin da ya sa kila ka dauki wannan matakin: Ka fahimci cewa iyayenka suna da iko a kanka kuma kana daukan shawarwarinsu da muhimmanci. (Kolosiyawa 3:20) Kana kaunar iyayenka kuma ba ka son ka bata musu rai ta wurin fita a boye. (Misalai 10:1) Hakan zai iya ba ka zarafin bayyana damuwarka wata rana.

 Sakamakon: Iyayenka za su san cewa kana kaunarsu kuma kana musu biyayya. Kuma idan suka ga cewa bukatarka daidai ne, za su iya ba ka izinin tafiya.

Dalilin da Ya Sa Iyaye Za Su Iya Ce A’a

Kamar masu tsaro na bakin rafi, iyayenka sun fi ka hangen nesa tare da sanin inda hadari yake

 Za a iya misalta dalili na farko haka: Dā so samu ne, za ka fi son ka yi iyo cikin ruwan da ake da ’yan tsaro kewaye. Me ya sa? Domin sa’ad da kake iyo cikin ruwa, ba za ka damu da hadari sosai ba. Amma ’yan tsaron za su yi saurin hango hadarin da ke tafe. Hakazalika, domin iyayenka suna da basira kuma kwarewa, za su iya hango hadarin da kai ba za ka iya gani ba. Nufin iyayenka daya ne da na ’yan tsaron bakin rafi, ba so suke su bata nishadinka ba, amma suna son su taimake ka ne ka guje wa hadarurrukan da za su hana ka jin dadi nan gaba.

 Ga kuma wani dalili: Iyayenka suna so su kāre ka sosai. Kauna ce ke sa su amince ko kuma su ki amincewa bisa ga yanayin. Sa’ad da ka nemi izinin yin wani abu, sukan yi tunani ko su ba da izinin kuma su fuskanci duk sakamakon da ke ciki. Za su yi na’am kuma su amince idan sun tabbata cewa babu wani hadarin da zai same ka.

Abin da Za Ka Yi Don A Rika Amincewa da Bukatarka

 Abin da za ka iya yi

 Gaskiya: Ka yi wa kanka tambaya: ‘Mene ne ainihin dalilin da ya sa nake son na je? Domin ina jin dadin ayyukan ne, ko kuma ina so ne dai na kasancewa da tsarana? Domin wata da nake sha’awarta za ta kasance a wajen ne?’ To ka gaya wa iyayenka gaskiyar. Su ma a dā matasa ne, kuma sun san ka sosai. Saboda haka, za su iya sanin ainihi dalilinka na yin haka. Za su ga gaskiyarka, kuma za ka amfana daga hikimarsu. (Misalai 7:1, 2) A wani sashe kuma, idan ba ka da gaskiya, zai yi wuya a yarda da kai kuma da kyar su kyale ka ka je.

 Lokaci: Kada ka dami iyayenka da neman izini sa’ad da suke dawowa daga aiki ko kuma sa’ad da suke tattauna wani batu. Ka yi musu magana sa’ad da suke a natse. Amma kada ka jira sai lokacin ya rage kadan sa’an nan ka matsa musu lamba su ba ka amsar. Iyayenka ba za su so su tsai da shawara da hanzari haka ba. Ka gaya musu tun da wuri, don su iya tsai da shawara mai kyau.

 Batun: Kada ka nuna musu cewa ka fi su wayo. Ka bayyana dalla-dalla abin da kake so ka yi. Iyaye ba sa jin dadin irin amsar nan “ban sani ba,” musamman ma idan suka tambaye ka cewa: “Su wa za su zo wajen?” “Akwai wani da ya manyanta da zai kasance a wajen?” ko kuwa “Yaushe za ka dawo gida?”

 Hali: Kada ka yi wa iyayenka kallon makiya. Ka dauke su kamar abokanka—domin a kashin gaskiya su abokanka ne. Idan kana daukan iyayenka kamar abokanka, ba za ka rika yin musu da su ba kuma za su hada kai da kai.

 Ka nuna wa iyayenka cewa ka manyanta kuma za ka bi shawararsu kuma za ka yi biyayya da shi. Idan ka yi haka, za su daraja ka. Wata rana kila su kyale ka ka je.