Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Zai Taimaka Min In Zabi Wanda Zan Bi Misalinsa?

Me Zai Taimaka Min In Zabi Wanda Zan Bi Misalinsa?

 Wata mai suna Haley ta ce: “Idan ina fama da wata matsala a makaranta, abin da yake taimaka min shi ne, yin tunani game da wani da nake so da ya taba fuskantar irin wannan matsalar. Kuma ina kokarin bin misalinsa. Idan kana da wanda kake bin misalinsa, hakan zai iya taimaka maka ka bi da matsalolinka a hanyar da ta dace.”

 Wanda kake bin misalinsa zai iya taimaka maka ka guji matsaloli kuma ka cim ma burinka. Sai dai, ya kamata ka zabi mutumin kirki da za ka bi misalinsa

 Me ya sa zai dace ka yi tunani kafin ka yi zabin?

  •   Za ka rika yin abubuwa kamar wanda kake so ka bi misalinsa.

     Littafi Mai Tsarki ya karfafa Kiristoci su rika lura da masu halin kirki sa’ad da ya ce: “Ku dubi karshensu, ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu.”​—Ibraniyawa 13:​7, Littafi Mai Tsarki.

     Taimako: Da yake wanda ka zaba ka bi misalinsa zai iya sa ka zama mutumin kirki ko a’a, ka zabi wadanda suke da halaye masu kyau sosai, kuma ba sai sun zama sanannu ko kuma tsararka ba.

     Wani mai suna Colin ya ce: “Na koyi abubuwa da yawa daga wurin abokina Adam. Yana da hankali kuma yana da halin sanin ya kamata. Abin mamakin shi ne, har yanzu ina tuna wasu abubuwan da ya fada da wadanda da ya yi. Shi da kansa ma bai san abubuwan nan sun taimaka min ba.”

  •   Halin mutanen da kake bin misalinsu zai iya shafan tunaninka da yadda kake ji.

     Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku yaudaru: zama da miyagu takan bata halaye na kirki.”​—1 Korintiyawa 15:33.

     Taimako: Ka zabi wadanda suke da halayen kirki, ba wadanda suke da kyaun fuska kawai ba. In ba ka yi haka ba, za ka iya fadawa cikin matsala.

     Wata mai suna Tamara ta ce: “Idan kana yawan gwada kanka da wadanda suke da kyau sosai, hakan zai sa ka rena kanka ko ka ga kamar ba ka kyau. Zai kuma sa ka rika mai da hankalinka ga yadda siffar jikinka yake.”

     Ka yi tunani a kan wannan: Me ya sa bin misalin wani fitaccen dan fim ko wasanni yake da hadari?

  •   Irin mutanen da kake so ka bi misalinsu za su iya taimaka maka ka cim ma burinka ko a’a.

     Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka yi tafiya tare da masu hikima, kai kuwa za ka yi hikima.”​—Misalai 13:20.:20.

     Taimako: Ka zabi wadanda suke da halayen da za ka so ka bi misalinsu. Yayin da kake ganin abubuwan da suke yi, hakan zai sa ka rika koyi da su kadan-kadan har sai ka cim ma burinka.

     Wata mai suna Miriam ta ce: “Maimakon kawai ka ce, ‘ina so ina zama da halin sanin ya kamata,’ zai fi ka ce, ‘zan so in zama da halin sanin ya kamata kamar Jane. Domin ba ta latti kuma ba ta wasa da aikinta.’”

     Gaskiyar al’amarin: Idan ka zabi mutumin da yake da halin kirki, za ka san yadda za ka bi da rayuwarka.

Bin misalin wani mutumin kirki zai iya taimaka maka ka cim ma burinka!

 Abin da zai taimaka maka

 Za ka iya zaban daya daga cikin biyun nan.

  1.   Za ka iya zaban irin halin da kake so ka koya, sa’an nan ka nemi wanda kake so da yake da irin wannan halin.

  2.   Za ka iya zaban wanda kake so ka bi misalinsa, sa’an nan ka zabi halin da kake so ka koya da daga wurin shi ko ita.

 Shafin rubutun da ke tare da wannan talifin zai taimaka maka ka yi hakan.

 Wadanda za ka iya zaba su ne:

  •  Tsararka. Wata mai suna Miriam ta ce: “Ina so in bi misalin abokiyata ta kud da kud ne. Ta damu da mutane sosai. Ko da yake na girme ta, amma tana da halaye masu kyau da ba ni da su, shi ya sa nake so in bi misalinta.”

  •  Wani da ya manyanta. Watakila iyayenka ne ko wani da addininku daya. Wata mai suna Annette ta ce: “Babu shakka, iyayena ne nake so in bi misalinsu. Suna da kyawawan halaye. Ko da yake suna kuskure wani lokaci, amma ina ganin yadda suke kokarin rike amincinsu ga Allah. Ina fatan idan na kai shekarunsu za a fadi hakan game da ni.”

  •  Wasu daga Littafi Mai Tsarki. Wata mai suna Melinda ta ce: “Na zabi wasu daga Littafi Mai Tsarki da nake so in bi misalinsu kuma su ne, Timotawus da Ruth da Ayuba da Bitrus da karamar ‘yar Isra’ila nan, ina da dalilin da na zabi kowannen su. Sa’ad da na ci gaba da karanta labarin su, sai na soma daukansu a matsayin abokaina. Na ji dadin karanta labaran su a littafi nan, Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu da kuma ‘Role Model Index’ da ke littafin nan, Questions Young People Ask​—Answers That Work.

 Taimako: Bai kamata ka ce mutum daya ne kawai za ka bi misalinsa ba. Manzo Bulus ya fada wa sauran Kiristocin cewa: “Ku duba wadannan da suke tafiya yadda muka zama abin koyi a gare ku.”​—Filibiyawa 3:17.

 Ka sani? Kai ma za ka iya zama abin koyi ga wani! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka zama gurbi ga masu ba da gaskiya, cikin magana, tasarrufi, kauna, bangaskiya, da tsabtar rai.”​—1 Timotawus 4:12.

 Wata mai suna Kiana ta ce: “Ko da kai ma kana kokarin bin misalin wasu, za ka iya taimaka wa wasu. Don ba ka san ko su waye ne suke kallonka ko suke jin abubuwan da kake furtawa ba. Hakan zai iya sa wani ya canja halinsa.”