Menene Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Dabbobin da Ake Kira Dinosaurs?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Babu wata aya da ta yi magana kai tsaye game da dinosaurs a Littafi Mai Tsarki. Ko da yake Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ne ya “halicci dukan abu,” hakika suna cikin dabbobin da ya halitta. a (Ruya ta Yohanna 4:11) Duk da cewa Littafi Mai Tsarki bai ambata sunan nan dinosaurs kai tsaye ba, ya ambata wasu halittu da watakila suka kunshi dabbar nan dinosaurs:
“Katayen abubuwa,” ko kuma “manyan dodanni.”—Farawa 1:21.
“Kowanne abin da ke rarrafe a kasa.”—Farawa 1:25.
“Dabbobi na duniya.”—Farawa 1:25.
Juyin halitta na wasu dabbobi ne ya kai ga wanzuwar dinosaurs?
Kasussuwan dinosaurs da aka gano sun nuna cewa dabbar ba ta wanzu a hankali kamar ta juyin halitta ba, amma ta fito ne farat daya. Wannan ya jitu da yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah ne ya halicci kowane dabba. Alal misali, Zabura 146:6 ya ce game da Allah cewa shi ne “Mai-halittan sama da kasa, da teku, da abin da ke cikinsu duka.”
A wanne lokaci ne dinosaurs suka wanzu?
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa an halicci dabbobin teku da na kasa a rana ta biyar da shida. b (Farawa 1:20-25, 31) Ta hakan, Littafi Mai Tsarki ya goyi bayan wanzuwar dinosaurs na dogon lokaci a duniya.
Behemoth da Leviathan dinosaurs ne?
A’a. Ko da yake wadannan dabbobin da aka ambata a littafin Ayuba ba za a iya gane su dai-dai ba, Behemoth dai an saba saninsa da suna dorinar-ruwa, kuma cewa Leviathan shi ne kada. Wadannan ra’ayoyin sun yi daidai da kwatancin da aka yi a cikin Littafi Mai tsarki. (Ayuba 40:15-23; 41:1, 14-17, 31) Wadannan sunayen “Behemoth” da “Leviathan” ba sa nufin dinosaurs. Me ya sa? Don Allah ya gaya wa Ayuba ya lura da wadannan dabbobin kuma a wannan lokacin, an gano cewa dinosaurs sun riga sun wanzu da dadewa kuma sun daina wanzuwa.—Ayuba 40:16; 41:8.
To me ya faru da Dinosaurs?
Littafi Mai Tsarki bai ce kome game da bacewar dinosaurs ba. Amma ya fadi cewa an halicce kome ne don ‘nufin Allah,’ saboda haka, akwai dalilin da ya sa Allah ya halicci dinosaurs. (Ruya ta Yohanna 4:11) Allah ya kyale su su shude ne sa’ad da nufinsa na halittar su ta cika.