Me Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Zaman Aure?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Da Allah ya gama halittar namiji da tamace na farko, shi ne ya hada su aure. Allah ya shirya aure don ya hada namiji da mace a hanya ta musamman kuma wannan dangantakar za ta zama kariya ga su da yaran da za su haifa.—Farawa 1:27, 28; 2:18.
Allah yana son maꞌaurata su ji dadin zama tare. (Karin Magana 5:18) Ya ba da shawarwari da kaꞌidodi a Littafi Mai Tsarki da za su taimaka wa mata da miji su ji dadin aurensu.
A wannan talifin, za mu bincika:
Yaya Allah yake so aure ya kasance?
Tun farko, Allah ya shirya aure ya kasance tsakanin namiji da mace guda ne. (Farawa 2:24) Allah ba ya son mutum ya auri mace fiye da daya kuma ya haramta luwadi da daudanci da madigo da kuma dadiro, wato zaman tare tsakanin namiji da ta mace ba tare da sun yi aure ba. (1 Tasalonikawa 4:3) Yesu ya ce wa mabiyansu su bi yadda Allah ya so aure ya kasance tun farko.—Markus 10:6-8.
A gun Allah, aure abu ne na din-din-din. A lokacin aure, namiji da macen sukan yi alkawarin cewa ba za su ci amanar juna ba kuma za su zauna tare duk rayuwarsu. Allah yana son su cika wannan alkawarin.—Markus 10:9.
Batun rabuwa da kashe aure kuma fa?
Wani lokaci mata da miji za su iya barin juna, watakila mutum daya ya yi tafiya don ya yi wani abu mai muhimmanci. Amma Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah ba ya son mata da miji su rabu don sun sami sabani ko don akwai matsala a tsakaninsu. A maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya ce su yi kokari su sasanta.—1 Korintiyawa 7:10.
Zina ce kadai za ta ba wa mutum dama ya kashe aurensa. (Matiyu 19:9) Saboda haka, idan mata da miji suka ce za su rabu ko su kashe aurensu ba don waninsu ya yi zina ba, Littafi Mai Tsarki bai yarda musu su yi aure ko su nemi wani ko wata ba, dole su zauna haka.—Matiyu 5:32; 1 Korintiyawa 7:11.
Shin sai dole an yi rajistar aure bisa doka kafin Allah ya amince da shi?
Allah yana son Kiristoci su rika bin doka kuma hakan ya hada da dokar kasa game da yin aure. (Titus 3:1) Don haka idan zai yiwu, maꞌaurata su yi rajistar aurensu bisa doka, hakan zai nuna cewa suna daraja hukuma da raꞌayin Allah cewa aure abu ne na din-din-din. a
Wane hakki ne Allah ya ba wa mata da miji?
Abin da Allah ke bukata daga su biyun. Allah ya ce mata da miji su nuna wa juna kauna kuma su girmama juna. (Afisawa 5:33) A batun jimaꞌi ya kamata su dinga biya ma juna bukata cikin kauna kuma su guji duk abin da zai sa su ci amana. (1 Korintiyawa 7:3; Ibraniyawa 13:4) Idan suna da yara, su biyun ne suke da hakkin tarbiyyartar da su.—Karin Magana 6:20.
Littafi Mai Tsarki bai yi bayani dalla-dalla a kan ko wane ne zai yi wani aiki a gida ba. Don haka, maꞌaurata ne za su tattauna kuma su tsai da shawarar da za ta fi musu alheri.
Hakkin miji ko maigida. Littafi Mai Tsarki ya ce “miji shi ne kan matarsa.” (Afisawa 5:23) Wato, ya kamata ya rika yi wa matarsa ja-goranci kuma ya tsai da shawarwari da za su amfani matarsa da yaransu.
Ya kamata ya yi iya kokarinsa ya kula da matarsa, ya tabbata cewa suna lafiya, suna samun kwanciyar hankali kuma sun kusaci Allah. (1 Timoti 5:8) Ya rika yin abubuwa tare da matarsa kuma ya rika tunani a kan ra’ayinta da yadda take ji kafin ya tsai da shawara, hakan zai nuna cewa bai rena ta ba kuma ya san cewa za ta iya taimaka masa. (Karin Magana 31:11, 28) Littafi Mai Tsarki ya ce mazaje su rika yin abubuwa da kauna.—Kolosiyawa 3:19.
Hakkin mace ko uwargida. Littafi Mai Tsarki ya ce mace “ta girmama mijinta.” (Afisawa 5:33) Allah yana farin ciki idan ya ga mace tana girmama maigidanta.
Hakkin da Allah ya ba ta shi ne ta dinga tallafawa maigidanta, don ya iya tsai da shawarwari masu kyau kuma ya yi ma iyalinsa ja-goranci. (Farawa 2:18) Baibul ya yaba wa matan da suke cika hakkinsu a aurensu.—Karin Magana 31:10.
A raꞌayin Allah, dole ne maꞌaurata a yau su haifi yara?
Aꞌa. A dā dai kam, Allah ya umurci wasu bayinsa su haifi ꞌyaꞌya. (Farawa 1:28; 9:1) Amma wannan dokar ba ta shafi Kiristoci ba. Yesu bai taba ba wa mabiyansa umurni su haifi ꞌyaꞌya ba. Mabiyansa na farko ma ba su ce dole ne maꞌaurata su haifi ꞌyaꞌya ba. Don haka, maꞌaurata ne za su tsai da shawara ko za su haifi ꞌyaꞌya ko aꞌa.
Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana da aurenmu?
Akwai shawarwari a Littafi Mai Tsarki da za su taimaka wa masu sabon aure sosai. Ban da haka, kaꞌidodin Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka wa maꞌaurata su kauce ma matsaloli ko su magance su.
Shawarar Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka wa maꞌaurata . . .
su nuna ma juna kauna ta gaskiya.—1 Korintiyawa 13:4-7; Kolosiyawa 3:14.
su dinga kyautata ma juna.—1 Korintiyawa 10:24.
su dinga saurarar juna.—Yakub 1:19.
su dinga girmama juna.—Romawa 12:10.
su dinga gafarta ma juna.—1 Bitrus 4:8.
su zama masu rikon amana.—Markus 10:9.
su zama masu hakuri.—Afisawa 4:2, 3.
su dinga yin abubuwa tare.—Mai-Waꞌazi 4:9.
su rike juna, ba rabuwa.—Wakar Wakoki 8:7.
a Don ganin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da auren alꞌada, karanta Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 2006, shafi na 21, sakin layi na 12.