Koma ka ga abin da ke ciki

Shin Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taꞌazantar da Ni Kuwa?

Shin Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taꞌazantar da Ni Kuwa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 E. (Romawa 15:4) Ka ga wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka taꞌazantar da mutane da yawa da suke fama da matsaloli ko kuma suna cikin wani yanayi mai wuya.

A wannan talifin, za mu tattauna:

 Shan wahala

 Zabura 23:4: “Ko da na bi ta ramin duhun mutuwa, ba zan ji tsoron kome ba, gama kana nan tare da ni.”

 Abin da hakan yake nufi: Idan ka yi adduꞌa ga Allah kuma ka dogara ga Kalmarsa Littafi Mai Tsarki don ya ja-gorance ka, za ka zama da karfin hali ko da kana cikin wani yanayi mai wuya.

 Filibiyawa 4:13: “Zan iya yin kome ta wurin Almasihu wanda yake karfafa ni.”

 Abin da hakan yake nufi: Allah zai taimake ka ka jimre kowace irin matsala.

 Idan wani da muke kauna ya mutu

 Mai-Waꞌazi 9:10: “Gama babu aiki, ko tunani, ko sani, ko hikima a wurin zaman matattu inda za ka tafi.”

 Abin da hakan yake nufi: Wadanda suka mutu ba sa shan wahala kuma ba za su iya yi mana lahani ba. Domin ba su san kome ba.

 Ayyukan Manzanni 24:15: “Za a tā da matattu.”

 Abin da hakan yake nufi: Allah zai ta da ꞌyanꞌuwanmu da abokanmu da suka mutu.

 Yawan bakin ciki don wani kuskuren da muka yi

 Zabura 86:5: “Gama kai, ya Ubangiji, mai alheri ne kuma mai yin gafara, mai yawan kauna marar canjawa ga dukan masu kira gare ka.”

 Abin da hakan yake nufi: Allah yana gafarta wa mutanen da suka tuba da gaske don zunubin da suka yi kuma suka kudura cewa ba za su sake ba.

 Zabura 103:​12, Mai Makamantu Ayoyi: “Kamar yadda gabas take nesa da yamma, haka nan ne ya nisantar da zunubanmu daga gare mu.”

 Abin da hakan yake nufi: Idan Allah ya gafarta wa mutum zunubi, yakan manta da zunubin. Ba ya shariꞌanta mutumin da zunubin ko ya hukunta shi da zunubin.

 Damuwa

 Zabura 31:7: “Gama ka ga wahalata, ka san damuwar zuciyata.”

 Abin da hakan yake nufi: Allah yana sane da famar da kake yi. Ya san yadda kake ji ko da mutane ba su fahimci hakan ba.

 Zabura 34:18: “Ga wadanda an karya musu karfin gwiwa, Yahweh a yana kusa da su, yakan kubutar da masu fid da zuciya.”

 Abin da hakan yake nufi: Allah ya yi alkawari cewa zai taimaka maka saꞌad da kake damuwa. Zai ba ka karfin jimrewa.

 Ciwo

 Zabura 41:3: “Yahweh zai . . . warkar da shi daga rashin lafiyarsa.”

 Abin da hakan yake nufi: Allah zai taimake ka ka jimre ciwon da kake yi ta wajen ba ka kwanciyar hankali, da karfin jimrewa da hikimar tsai da shawarwari.

 Ishaya 33:24: “Ba mazaunin kasar da zai ce, ‘Ina ciwo.’”

 Abin da hakan yake nufi: Allah ya yi alkawari cewa a nan gaba, dukan mutane za su more koshin lafiya.

 Gajiya da dawainiya

 Zabura 94:19: “Saꞌad da damuwoyi sukan yi mini yawa, taꞌaziyyarka takan karfafa raina.”

 Abin da hakan yake nufi: Idan muka yi adduꞌa ga Allah saꞌad da muke cikin damuwa, zai taimaka mana mu natsu.

 1 Bitrus 5:7: “Ku danka masa dukan damuwarku, gama shi ne mai lura da ku.”

 Abin da hakan yake nufi: Allah ya damu da wahalar da muke sha. Ya ce mu yi adduꞌa mu gaya masa duk abin da ke damunmu.

 Saꞌad da ake yaki

 Zabura 46:9: “Ya tsai da yake-yake a dukan duniya.”

 Abin da hakan yake nufi: Mulkin Allah zai kawar da yaki gabaki daya nan ba da dadewa ba.

 Zabura 37:​11, 29: “Masu saukin kai za su gāji kasar, su sami farin cikinsu cikin salama a yalwace. . . . Masu adalci za su gāji kasar, su zauna a ciki har abada.”

 Abin da hakan yake nufi: Mutanen kirki za su more salama a duniya har abada.

 Damuwa game da nan gaba

 Irmiya 29:11: “Na san irin shirin da nake da shi domin ku. Shiri ne na alheri, ba na masifa ba, domin in ba ku sa zuciya da rayuwa ta nan gaba. Ni Yahweh na fada.”

 Abin da hakan yake nufi: Allah ya tabbatar wa mutanen sa cewa abubuwa za su gyaru a nan gaba.

 Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4: “Zai share musu dukan hawaye daga idanunsu. Babu sauran mutuwa, ko bakin ciki, ko kuka, ko azaba. Gama abubuwan dā sun bace.”

 Abin da hakan yake nufi: Allah ya yi alkawari cewa zai kawar da munanan abubuwan da suke faruwa a yau.

a Jehobah ko Yahweh shi ne sunan Allah. (Zabura 83:18) Ka karanta talifin nan “Wane ne Jehovah?