Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Ramako?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Ko da mutum yana ganin kamar ya kamata ya rama abin da aka yi masa, yin hakan bai jitu da umurnin Littafi Mai Tsarki da ya ce: “Kada ka ce, ‘Ni ma zan yi masa yadda shi ya yi mini, zan rama abin da ya yi mini.’ ” (Karin Magana 24:29) A cikin Littafi Mai Tsarki akwai shawarwarin da suka taimaka wa mutane da yawa su daina neman damar rama abin da aka yi musu.
A wannan talifin za mu ga
Me ya sa bai da kyau mu yi ramako?
Idan wani ya bata maka rai ko ya ji maka ciwo, ba shakka za ka ji haushi kuma za ka so a hukunta shi ko ita don abin da ta yi. Amma, yin ramako bai jitu da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce ba. Me ya sa?
Idan ꞌyan Adam suna ramako, hakan yana bata ran Allah. A Littafi Mai Tsarki Jehobah a ya ce: “Ramuwa tawa ce, ni kuwa zan rama, in ji Ubangiji.” (Romawa 12:19) Littafi Mai Tsarki ya shawarci wadanda aka wulakanta su, su nemi yadda za su sasanta matsalar cikin salama maimako su rama. (Romawa 12:18) Amma mene ne mutum zai iya yi, idan ya yi kokarin sasanta matsala cikin salama kuma hakan ya gagara? Littafi Mai Tsarki ya umurce mu mu dogara da abin da Jehobah zai yi don ya kawo karshen rashin adalci.—Zabura 42:10, 11.
Ta yaya Allah yake hukunta mutane?
A yanzu, Allah yana barin hukumomin gwamnati su hukunta masu laifi. (Romawa 13:1-4) Nan ba da dadewa ba, zai hukunta mugaye, zai kuma tabbata cewa babu wanda zai kara shan wahala.—Ishaya 11:4.
Ta yaya zan daina neman damar rama abin da aka yi mini?
Ka guji daukan mataki don kana fushi. (Karin Magana 17:27) Sau da yawa mutane da suke daukan mataki don suna fushi, suna da-na-sani. Amma, wadanda suke yin tunani kafin su dauki mataki, za su fi yanke shawarwari masu kyau.—Karin Magana 29:11.
Ka san gaskiyar lamarin. (Karin Magana 18:13) Idan aka yi maka laifi, zai dace ka tambayi kanka cewa, shin akwai dalilin da ya sa aka yi mini hakan da ban sani ba? Ko akwai abin da ke damunsa? Ko kuma ya yi abin ba tare da saninsa ba ne? A wasu lokuta, za mu iya gani kamar mutumin ya yi mana laifi da gangan, amma da gaske kuskure ne ya yi.
Karya game da ramako
Karya: Littafi Mai Tsarki ya umurce mu mu yi ramako, da ya ce idan mutum ya “cire wa wani ido, shi ma za a cire nasa idon.”—Littafin Firistoci 24:20.
Gaskiya: A Israꞌila ta dā, an kafa dokar da ta ce idan mutum ya “cire wa wani ido, shi ma za a cire nasa idon” don a hana mutane yin ramako da kansu. Kuma dokar ta taimaka wa alkalai su hukunta mutanen da suka yi laifi yadda ya dace. b—Maimaitawar Shari’a 19:15-21.
Karya: Da yake Littafi Mai Tsarki bai umurce mu yi ramako ba, ba za mu iya kāre kanmu ba idan aka kawo mana hari.
Gaskiya: Idan aka kawo mana hari, mutum zai iya kāre kansa ko ya nemi taimakon hukumomi. Amma Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa kada mu yi fada da mutane.—Karin Magana 17:14.
a Jehobah ne sunan Allah kamar yadda aka nuna a Littafi Mai Tsarki.
b Don samun cikakken bayani game da dokar nan, ka duba talifin nan “Mene ne Ma’anar Furucin Nan ‘Ido a Maimakon Ido’?”