Mene ne Idin Ketarewa?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Idin Ketarewa biki ne da Yahudawa suke yi domin ’yancin da Allah ya ba su daga bauta a kasar Masar a shekara ta 1513 kafin haihuwar Yesu. Allah ya umurci Isra’ilawa cewa su rika tunawa da wannan rana mai muhimmanci kowace shekara kuma su rika yin hakan a ranar 14 ga watan Abib na Yahudawa, wanda daga baya aka fi sani da sa Nisan.—Fitowa 12:42; Levitikus 23:5.
Me ya sa ake kiran sa Idin Ketarewa?
Furucin nan “Idin Ketarewa” yana nufin lokacin da Allah ya kāre Isra’ilawa daga bala’in da ya kashe dukan ’ya’yan fari na Masarawa. (Fitowa 12:27; 13:15) Kafin wannan annobar ta auku, Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa su yanka rago ko akuya, sai su yafa jinin a jikin kofar gidansu. (Fitowa 12:21, 22) Sa’ad da Allah ya “ketare” gidansu kuma ya ga alamar, sai ya kyale ’ya’yan farinsu da rai.—Fitowa 12:7, 13.
Yaya ake yin Idin Ketarewa a zamanin dā?
Allah ya gaya wa Isra’ilawa dalla-dalla yadda za su yi Idin. a Ga wasu abubuwan da ake yi a lokacin Idin Ketarewa.
Hadaya: Iyalai sukan zabi rago (ko akuya) da ya kai shekara daya a ranar goma ga watan Abib (Nisan), sa’an nan su yanka shi a ranar 14th ga watan. A rana ta farko da Yahudawa suka fara yin Idin Ketarewa, sun yafa jinin ragon a jikin kofar gidansu kuma suka gasa sauran naman suka ci.—Fitowa 12:3-9.
Abinci: Bayan naman rago (ko akuya) da suke yankawa, Isra’ilawan suna cin burodi mara yisti da kuma ganye mai daci a ranar Idin.—Fitowa 12:8.
Idi: Isra’ilawan sukan yi Idin Gurasa Mara Yisti har na kwana bakwai bayan Idin Ketarewa, kuma a wannan lokacin ba sa cin gurasa mai yisti.—Fitowa 12:17-20; 2 Labarbaru 30:21.
Koyarwa: Iyaye sukan yi amfani da lokacin Idin Ketarewa don su koya wa yaransu game da Jehobah.—Fitowa 12:25-27.
Tafiye-Tafiye: Daga baya, Isra’ilawa sukan yi tafiya zuwa Urushalima don su yi Idin Ketarewa.—Kubawar Shari’a 16:5-7; Luka 2:41.
Wasu abubuwan da suke yi: A zamanin Yesu, akan yi wake-wake kuma akan sha ruwan inabi a lokacin Idin.—Matta 26:19, 30; Luka 22:15-18.
Karya game da Idin Ketarewa
Karya: Isra’ilawa suna cin abincin Idin Ketarewa a ranar 15 ga Nisan.
Gaskiya: Allah ya gaya wa Isra’ilawa su yanka rago bayan faduwar rana a ranar 14 ga Nisan kuma su ci naman a daren. (Fitowa 12:6, 8) Isra’ilawa sukan fara kirga kwanakinsu bayan faduwar rana. (Levitikus 23:32) Saboda haka, Isra’ilawan sun ci abincin Idin a farawar 14 ga Nisan.
Karya: Ya kamata Kiristoci su yi Idin Ketarewa.
Gaskiya: Bayan Yesu ya yi Idin Ketarewa a ranar 14 ga Nisan shekara ta 33 bayan haihuwarsa, ya kafa wata sabuwar Idi: Jibin Maraice na Ubangiji. (Luka 22:19, 20; 1 Korintiyawa 11:20) Wannan ya maye gurbin Idin Ketarewa, domin yana tuna mana da hadayar da Kristi ‘Dan Rago na Idin Ketarewa’ ya yi. (1 Korintiyawa 5:7) Hadayar da Yesu ya yi ta fi na Idin Ketarewa, domin ta fanshe dukan mutane daga zunubi da kuma mutuwa.—Matta 20:28; Ibraniyawa 9:15.
a Daga baya an yi wasu canje-canje da ya kamata. Alal misali, Isra’ilawan sun yi bikin cikin gaggawa domin suna kokarin barin kasar Masar. (Fitowa 12:11) Amma da suka isa Kasar Alkawari, ba sa bukatar su yi Idin cikin gaggawa kuma.