Mene ne Yake Nufi Mutum ya Zama Mai Tsarki?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Mutum ya zama mai tsarki yana nufin ba zai sa hannu a duk wani abin da zai kazantar da shi ba. An dauko kalmar Ibrananci da aka fassara zuwa “tsarki” daga furucin da ke nufin “ware” wani abu.Saboda haka, abu mai tsarki abu ne da aka ware ko kuma kebe, musamman ma don yana da tamani da kuma tsabta.
Allah ne ya fi tsarki. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji.” a (1 Sama’ila 2:2) Saboda haka, Allah ne ke da izinin kafa mizani na abu mai-tsarki.
Za a iya yin amfani da kalmar nan “tsarki” a duk abin da ya shafi Allah, musamman ma abubuwan da aka kebe su domin sujada. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da:
Wurare masu tsarki: Allah ya yi magana da Musa a kusa da kurmin da ke ci da wuta ya ce: “Wurin da kake tsayawa wuri mai-tsarki ne.”—Fitowa 3:2-5.
Taro masu tsarki: Isra’ilawa na dā sun yi taro don bauta wa Allah kuma suka kira hakan taro “masu tsarki.”—Levitikus 23:37.
Kayayyaki masu tsarki: Ana kiran kayayyakin da aka yi amfani da su domin sujada ga Allah a Urushalima “kayayyaki masu tsarki.” (1 Sarakuna 8:4) An bukaci a rika daraja wadannan kayayyaki masu tsarki, ko da yake ba za a yi masu sujada ba. b
Shin mutum ajizi zai iya zama mai-tsarki?
E. Allah ya umurci Kiristoci: “Sai ku zama tsarkaka domin ni mai tsarki ne.” (1 Bitrus 1:16) Hakika, mutane ajizai ba za su iya zama kamiltattu kamar yadda Allah yake ba. Duk da haka, ana daukan mutanen da suka kiyaye dokokin Allah “tsattsarka, abar karɓa ga Allah.” (Romawa 12:1) Duk wanda yake kokarin ya zama mai-tsarki yana nunawa a furucinsa da ayyukansa. Alal misali mutumin yana bin shawarar Littafi Mai Tsarki da ta ce “ku yi zaman tsarki, ku guje wa fasikanci,” da kuma “ku ma kanku sai ku zama tsarkaka cikin dukan al’amuranku.”—1 Tasalonikawa 4:3; 1 Bitrus1:15.
Shin za a iya kasancewa da rashin tsarki a gaban Allah?
E. Duk wanda ya ki bin mizanan Allah, mutumin ba zai kasance da tsarki a gaban Allah ba. Alal misali Littafin Ibraniyawa ya yi magana game da “’yan’uwa tsarkaka,” kari ga haka ya yi masu kashedi cewa “kada wata muguwar zuciyar marar gaskatawa ta wakana ga waninku, wadda za ta bauɗar da ku daga wurin Allah Rayayye.” —Ibraniyawa 3:1, 12.
Ra’ayin da bai dace ba game da zama mai-tsarki
Ra’ayi: Mutum yana iya zama mai tsarki ta wurin hana zuciyarsa abin da take bukata.
Gaskiyar: Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa “wahalar da jiki” ko kuwa hana zuciya abin da take bukata, “ba ta da amfani” a wurin Allah. (Kolosiyawa 2:23) A maimakon haka, Allah na son mu ji dadin abubuwa masu kyau. “Dukanmu mu ci, mu sha, mu yi murna da abin da muka yi aikinsa, gama wannan kyautar Allah ce.”—Mai-Wa’azi 3:13.
Ra’ayi: Kin yin aure zai sa mutum ya kara zama mai-tsarki
Gaskiyar: Kirista ne zai yanke wa kansa shawarar yin aure ko a’a, ko mutum ya yi aure ko bai yi ba, hakan ba hanya ce na kasancewa da tsarki a gaban Allah ba. Gaskiya ne cewa wadanda suka zabi su zauna babu aure za su iya ba da hankulansu ga aikin ibada sosai. (1 Korintiyawa 7:32-34) Ban da haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa masu aure ma za su iya kasancewa da tsarki. Daya daga cikin manzannin Yesu wato Bitrus na da aure.—Matta 8:14; 1 Korintiyawa 9:5.