Me Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Kula da Iyaye da Suka Tsufa?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Yaran da suka yi girma ne suke da hakkin kula da iyayensu da suka tsufa. Littafi Mai Tsarki ya ce yaran da suka yi girma “su fara koyon nuna hali irin na Allah ga danginsu, domin ta haka su ma za su mayar wa iyayensu taimakon da suka samu daga gare su. Gama wannan ya faranta wa Allah rai.” (1 Timoti 5:4) Idan yara suna kula da tsofaffinsu kuma suna biya musu bukata, wannan zai nuna cewa suna bin dokar Allah da ta ce yara su girmama iyayensu.—Afisawa 6:2, 3.
Littafi Mai Tsarki bai gaya mana abubuwan da za mu yi don mu kula da iyayenmu da suka tsufa ba. Amma ya ba mu labarin bayin Allah da suka yi hakan. Ban da haka ma, ya ba da shawarwari da za su taimaka ma wadanda suke kula da tsofaffinsu.
Mene ne bayin Allah a dā suka yi don su kula da tsofaffinsu?
Da yake yanayinsu ba daya ba ne, sun bi hanyoyi dabam-dabam don su kula da iyayensu.
Yusufu ya yi zama a gari da ke da nisa da inda babansa mai suna Yakubu yake. Amma da ya sami dama, ya kawo mahaifinsa ya zo ya zauna kusa da shi. Ya samo wa mahaifinsa inda zai zauna, ya ciyar da shi, kuma ya tabbatar da lafiyarsa.—Farawa 45:9-11; 47:11, 12.
Rut ta bi surkuwarta zuwa kasarsu kuma ta yi aiki sosai don ta kula da ita.—Rut 1:16; 2:2, 17, 18, 23.
Yesu kuma da ya ga cewa za a kashe shi, ya ce ma wani manzonsa mai suna Yohanna ya kula da Maryamu, mahaifiyarsa. Da alama cewa a wannan lokacin, maigidanta ya riga ya rasu.—Yohanna 19:26, 27. a
Wace shawarar Littafi Mai Tsarki ce za ta taimaka wa masu kula da tsofaffi?
Kula da iyayenmu da suka tsufa abu ne da ba shi da sauki, amma shawarar Littafi Mai Tsarki, za ta iya taimaka mana mu yi hakan da kyau.
Ka girmama iyayenka.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka girmama babanka da mamarka.”—Fitowa 20:12.
Ta yaya za ka bi wannan shawarar? Ka girmama iyayenka ta wajen barin su su yi abubuwa yadda suke so idan zai yiwu. Idan zai yiwu ka bar su su zabi yadda za a rika kula da su. Kari ga haka, ka yi abin da za ka iya yi don ka taimaka musu, hakan zai nuna cewa kana girmama su.
Ka yi kokari ka fahimce su kana gafarta musu.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Hankali yakan sa mutum ya danne fushinsa, kyale laifin da aka yi masa, abu ne mai kawo masa daraja.”—Karin Magana 19:11.
Ta yaya za ka bi wannan shawarar? Idan wanda kake kula da shi ba ya kyautata maka ko ba ya ganin kokarin da kake yi, ka tambayi kanka, ‘A ce ni ne na tsufa haka kuma ina wannan yanayin, yaya zan ji?’ Idan kana kokari ka fahimce su kuma kana gafarta musu, za ka kyautata zamanku.
Kada ka yi kome kai kadai.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan babu shawara, shiri yakan lalace, amma tare da shawara mai yawa, akwai cin nasara.”—Karin Magana 15:22.
Ta yaya za ka bi wannan shawarar? Tsofaffi sukan yi fama da rashin lafiya iri-iri. Don haka, ka yi bincike don ka san abin da za ka yi don ka taimaka musu. Ka yi bincike ko ka yi tambaya ka san ko akwai abin da gwamnati take yi don ta taimaka wa irinsu. Ka nemi shawara daga wurin wadanda suka taba kula da tsofaffinsu. Idan kana da ’yan’uwa, ku hadu ku yi shawara a kan yadda za ku biya bukatun iyayenku kuma ku kula da su.
Ka san kasawarka.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai saukin kai mai hikima ne.”—Karin Magana 11:2.
Ta yaya za ka bi wannan shawarar? Ka tuna cewa ba kome ne za ka iya yi ba. Ba mu da lokaci da kuma karfin yin duk abin da muke so. Don haka, idan ka ga cewa aiki yana so ya fi karfinka, ka nemi taimako daga wurin ’yan gidanku, ko kuma ka nemi shawara daga wurin wani da kake ganin zai iya taimaka maka.
Ka kula da kanka.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba wanda ya taba kin jikinsa, sai dai ya ciyar da shi ya kula da shi sosai.”—Afisawa 5:29.
Ta yaya za ka bi wannan shawarar? Ka tuna cewa ko da yake kana da hakkin kula da iyayenka, hakan ba ya nufin za ka manta da kanka da kuma iyalinka idan kana da aure. Ya kamata ka dinga cin abinci da kyau. Ka dinga hutawa kuma ka sami isasshen barci. (Mai-Wa’azi 4:6) Maimakon a ce kullum kai ne kake kula da su, ka shirya yadda wani zai karbe ka don ka samu ka huta. Idan kana yin wadannan abubuwan, za su kara maka karfin kula da iyayenka yadda ya kamata.
Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce a kan hanyar da ya kamata yara su kula da tsofaffinsu?
Littafi Mai Tsarki bai gaya mana dalla-dalla abin da za mu yi don mu kula da iyayenmu ba. A wasu gidaje, yaran da suka yi girma sukan kula da iyayensu da kansu, ko a gidansu ko a gidan iyayen. A wasu lokuta kuma, idan suka ga ba za su iya ba, sukan nemo wani ko wata ta dinga kula da iyayensu. Iyalin gabaki daya za su iya haduwa su tattauna hanya da za ta fi dacewa don su kula da tsofaffinsu.—Galatiyawa 6:4, 5.
a Wani littafi da ya yi bayani a kan wannan labarin ya ce: “Da alama cewa Yusufu [maigidan Maryamu] ya riga ya rasu da dadewa kuma danta Yesu ne yake kula da ita. Yanzu da za a kashe shi, wa zai kula da ita? . . . Abin da Yesu ya yi a nan, ya koya wa yara cewa ya kamata su dinga kula da iyayensu da suka tsufa.”—The NIV Matthew Henry Commentary in One Volume, shafuffuka na 428-429.