Yadda Za Mu Yi Adduꞌa—Maimaita Adduꞌar Ubangiji Ne Ya Fi?
Amsar Littafi Mai Tsarki
A adduꞌar Ubangiji, an nuna mana misalin yadda ya kamata mu yi adduꞌa da abin da za mu yi adduꞌa a kai. Yesu ya nuna wannan misalin saꞌad da almajiransa suka roke shi cewa: “Ubangiji ka koya mana yadda za mu yi adduꞌa.” (Luka 11:1) Duk da haka, Adduꞌar Ubangiji ba shi kadai ba ne adduꞌar da Allah yake ji. a Maimakon haka, adduꞌar misali ne da Yesu ya bayar don ya nuna mana irin adduꞌoꞌin da Allah yake amincewa da su.
A wannan talifin
Mene ne aka fada a cikin Adduꞌar Ubangiji?
An rubuta Adduꞌar Ubangiji da ke Matiyu 6:9-13 a hanyoyi dabam-dabam a juyin Littafi Mai Tsarki da dama. Ga misalai biyu.
New World Translation: “Ubanmu wanda yake cikin sama, a tsarkake sunanka. Mulkinka ya zo, bari a yi nufinka a cikin duniya, kamar yadda ake yinsa a cikin sama. Ka ba mu abincin yau da kullum. Ka yafe mana basusukanmu, kamar yadda muka yafe wa wadanda muke bi bashi. Kada ka kai mu cikin jarraba, amma ka tsare mu daga mugun nan.”
Juyi Mai Fitar da Maꞌana: “Ubanmu wanda yake cikin sama, a kiyaye sunanka da tsarki. Mulkinka ya zo, bari a yi nufinka a cikin duniya, kamar yadda ake yinsa a cikin sama. Ka ba mu abincin yau da kullum. Ka gafarta mana laifofinmu, kamar yadda muke gafarta wa waɗanda suke yi mana laifi. Kada ka kai mu cikin jarraba, amma ka tsare mu daga Mugun nan.”
Mene ne maꞌanar Adduꞌar Ubangiji?
Koyarwar Yesu ta jitu da abin da aka fada a cikin Nassosi, saboda haka, sauran sassan Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu fahimci maꞌanar Adduꞌar Ubangiji.
“Ubanmu wanda yake cikin sama”
Ya dace mu kira Allah “Ubanmu” domin shi ne ya halicce mu kuma ya ba mu rai.—Ishaya 64:8.
“A tsarkake sunanka”
Ya kamata a rika daraja sunan Allah Jehobah, a dauke shi da tsarki ko kuma a tsarkaka shi. ꞌYan Adam suna tsarkake sunan Allah a duk lokacin da suke gaya wa mutane game da halayensa da kuma nufe-nufensa.—Zabura 83:18; Ishaya 6:3.
“Mulkinka ya zo”
Mulkin Allah gwamnati ce da ke sama kuma Yesu ne Sarkinsa. Yesu ya koya mana mu yi adduꞌa wannan gwamnatin ta yi sarauta bisa dukan duniya.—Daniyel 2:44; Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 11:15.
“Bari a yi nufinka a cikin duniya, kamar yadda ake yinsa a cikin sama”
Kamar yadda ba a yin mugunta ko mutuwa a sama, nufin Allah wa duniya shi ne ꞌyan Adam su yi rayuwa har abada cikin salama da kwanciyar hankali.—Zabura 37:11, 29.
“Ka ba mu abincin yau da kullum”
Zai dace mu rika tuna cewa ya kamata mu dogara ga Mahaliccinmu ne don ya ba mu abubuwan da muke bukata.—Ayyukan Manzanni 17:24, 25.
“Ka yafe mana basusukanmu, kamar yadda muka yafe wa wadanda muke bi bashi”
A wannan ayar, kalmar nan “basusukanmu” tana nufin zunubai. (Luka 11:4) Dukan ꞌyan Adam suna zunubi kuma suna bukata a gafarta musu. Amma idan muna so Allah ya gafarta mana, wajibi ne mu gafarta wa mutane laifofin da suka yi mana.—Matiyu 6:14, 15.
“Kada ka kai mu cikin jarraba, amma ka tsare mu daga mugun nan”
Jehobah ba ya jarraba mu mu yi abin da bai dace ba. (Yakub 1:13) Amma “mugun nan” ko kuma “mai gwadawan nan,” wato Shaidan Iblis ne yake jarraba mu. (1 Yohanna 5:19; Matiyu 4:1-4, Mai Makamantu Ayoyi) Muna rokon Jehobah ya taimaka mana kada mu yi masa rashin biyayya saꞌad da aka jarraba mu.
Maimaita Adduꞌar Ubangiji hanya ce kadai da ya dace mu yi adduꞌa?
Yesu ya koyar da Adduꞌar Ubangiji don ya nuna misalin yadda ya kamata a yi adduꞌa. Bai kamata mu rika maimaita shi kalma bayan kalma ba. Kafin Yesu ya ba da misalin Adduꞌar Ubangiji, ya yi mana gargadi cewa: “In kuwa kuna adduꞌa, kada ku yi ta maimaitawar banza.” (Matiyu 6:7, Mai Makamantu Ayoyi) A wani lokaci, saꞌad da yake nuna wa mutane yadda ake adduꞌa, ya yi amfani da kalmomi dabam.—Luka 11:2-4.
Hanya mafi kyau na yin adduꞌa ita ce mu gaya wa Allah abin da muke tunaninsa da kuma yadda muke ji da dukan zuciyarmu.—Zabura 62:8.
Yaya ya kamata mu rika yin adduꞌa?
A Adduꞌar Ubangiji, an nuna mana misali mai kyau na yadda za mu yi adduꞌa don Allah ya saurare mu. Ka lura da yadda adduꞌar ta jitu da sauran ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka yi magana game da adduꞌa.
Ka rika adduꞌa ga Allah kadai
Nassi: “A cikin kome ku fada wa Allah bukatunku ta wurin addu’a da roko, tare da godiya.”—Filibiyawa 4:6.
Maꞌana: Ya kamata mu rika adduꞌa ga Allah kadai, ba ga Yesu ko Maryamu ko kuma waliyyai ba. Ta wurin kalmar nan “Ubanmu” da aka soma Adduꞌar Ubangiji da ita, an koya mana cewa ya kamata mu rika yin adduꞌa ga Jehobah ne kadai.
Ka rika adduꞌa don abubuwa da suka jitu da nufin Allah
Nassi: “Idan mun roki kome bisa ga nufinsa, zai saurare mu.”—1 Yohanna 5:14.
Maꞌana: Muna iya yin adduꞌa a kan kome da ya jitu da nufin Allah. Yesu ya nuna mana muhimmancin yin nufin Allah saꞌad da ya ce “bari a yi nufinka.” Za mu iya sanin nufin Allah wa duniya da kuma ꞌyan Adam ta wurin nazarin Littafi Mai Tsarki.
Ka yi adduꞌa game da abubuwan da ke damunka
Nassi: “Danka wa Yahweh damuwarka, shi kuwa zai lura da kai.”—Zabura 55:22.
Maꞌana: Allah ya damu da matsalolinmu. Yesu ya ambata bukatu da yawa na ꞌyan Adam a Adduꞌar Ubangiji. Mu ma za mu iya yin adduꞌa don Allah ya biya bukatunmu na yau da kullum, ya taimaka mana saꞌad da muke tsai da shawarwari masu muhimmanci da saꞌad da muke neman taimako, kuma ya gafarta mana zunubanmu. b
a Alal misali, a wasu adduꞌoꞌi da Yesu da almajiransa suka yi, ba su yi amfani da kalmomi da batutuwa da aka yi amfani da su a Adduꞌar Ubangiji ba.—Luka 23:34; Filibiyawa 1:9.
b Zuciyar wadanda sun yi zunubi za ta iya damun su har ta hana su yin adduꞌa. Amma Jehobah yana gaya musu cewa: “Ku zo mu shirya tsakaninmu.” (Ishaya 1:18) Ba zai ki gafarta wa duk wanda ya nemi gafararsa ba.