Me Ya Sa Aka Kira Yesu Dan Allah?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Sau da yawa an kira Yesu “Dan Allah” a cikin Littafi Mai Tsarki. (Yohanna 1:49) Furucin nan “Dan Allah” ya nuna cewa Allah ne Mahalicci ko kuma Tushen dukan rai, har da na Yesu. (Zabura 36:9; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11) Littafi Mai Tsarki bai ce Allah ya haifi Yesu yadda ’yan Adam suke haifan yara ba.
Littafi Mai Tsarki ya kira mala’iku ’ya’yan Allah. (Ayuba 1:6) Littafi Mai Tsarki ya ce Adamu mutum na farko “dan Allah” ne. (Luka 3:38) Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu Dan Allah ne na musamman domin shi ne Allah ya fara halitta kuma ya halicce shi kai tsaye ba tare da taimakon kowa ba.
Yesu yana sama ne kafin a haife shi a duniya?
E. Yesu ruhu ne a sama kafin a haife shi a duniya. Yesu ya ce: “Na sauko daga sama.”—Yohanna 6:38; 8:23.
Allah ya halicci Yesu kafin ya halicci kome. Littafi Mai Tsarki ya ce game da Yesu:
“Shi ne Dan fari gaban dukan halitta.”—Kolosiyawa 1:15.
“Ta wurinsa dukan halittar Allah ta kasance.”—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 3:14.
Yesu ya cika annabci game da “wanda asalinsa daga zamanin dā ne, daga kwanakin dā yake.”—Mika 5:2; Matiyu 2:4-6.
Mene ne Yesu ya yi kafin ya zo duniya?
Yana da matsayi mai girma a sama. Yesu ya yi maganar matsayinsa sa’ad da ya yi addu’a cewa: “Ya Uba, ka ɗaukaka ni da ɗaukakar nan da nake da ita a gabanka tun kafin halittar duniya.”—Yohanna 17:5.
Ya taimaka wa Ubansa da halittar dukan sauran abubuwa. Yesu ya yi aiki tare da Allah “kamar gwanin aiki.” (Karin Magana 8:30) Littafi Mai Tsarki ya ce game da Yesu: “Ta wurinsa ne aka yi kome da kome, abubuwan da suke a sammai da kuma a nan duniya.”—Kolosiyawa 1:16.
Ta wurin Yesu ne Allah ya halicce kome. Hakan ya kunshi dukan mala’iku, da kuma sama da kasa. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 5:11) A wasu hanyoyi, ana iya kwatanta hadin kai da ke tsakanin Allah da Yesu da na mai zanen gida da magini. Mai zanen ne ke zana irin gidan da za a gina; amma magini ne zai gina gidan.
Shi ne Kalman. A Littafi Mai Tsarki an kira Yesu “Kalman” sa’ad da ake magana game da shi kafin ya zo duniya. (Yohanna 1:1) Babu shakka, hakan yana nufin cewa Allah ya yi amfani da Dansa don ya ba sauran mala’iku umurni.
Kari ga haka, kamar dai ta bakin Yesu ne Allah ya yi wa ’yan Adam magana a duniya. Watakila Allah ya yi magana ta bakin Yesu sa’ad da yake ba Adamu da Hauwa’u umurni a lambun Adnin. (Farawa 2:16, 17) Watakila Yesu ne mala’ikan da ya ja-goranci Isra’ilawa a lokacin da suke tafiya a jeji kuma mai yiwuwa muryarsa ce suka ji.—Fitowa 23:20-23. a
a Allah bai yi magana ta wurin Kalman kadai ba. Alal misali, ya yi amfani da wasu mala’iku don ya ba Isra’ilawa a dā umurni, ba Dansa na fari kadai ba.—Ayyukan Manzanni 7:53; Galatiyawa 3:19; Ibraniyawa 2:2, 3.