Koma ka ga abin da ke ciki

29 GA SATUMBA, 2020
Azerbaijan

Kotun Turai na Kāre ’Yancin ’Yan Adam Ya Goyi Bayan Shaidun Jehobah a Azerbaijan a Hukunci Guda Biyu

Kotun Turai na Kāre ’Yancin ’Yan Adam Ya Goyi Bayan Shaidun Jehobah a Azerbaijan a Hukunci Guda Biyu

Kotun Turai na Kāre ’Yancin ’Yan Adam (wato ECHR) ya yanke hukunci guda biyu a ranar 24 ga Satumba, 2020, da suka nuna cewa kotun ya goyi bayan Shaidun Jehobah a Azerbaijan. Hukunci na farko a kan karar da aka shigar mai jigo, Valiyev and Others v. Azerbaijan ne, na biyu kuma mai jigo, Religious Community of Jehovah’s Witnesses v. Azerbaijan. Wadannan hukuncin sun kāre ’yancin da ’yan’uwanmu suke da shi na yin ayyukan ibada.

Sa’ad da ake sauraron kararrakin, gwamnatin Azerbaijan ta sanar da cewa ta tāke ’yancin ’yan’uwanmu. Gwamnatin ta kuma yarda cewa za ta biya ’yan’uwanmu diyyar dala 22,146 (wajen naira 8,481,918). Hukuncin da ECHR ya yanke ya nuna cewa Kotun ya amince da wannan sanarwar da gwamnatin Azerbaijan ta yi.

Dan’uwa Valiyev yana jawabi a taro a wani gida

A 2011 ne aka shigar da karar nan mai jigo, Valiyev and Others v. Azerbaijan a kotun ECHR, kuma karar saboda ’yan’uwanmu da ke birnin Ganja ne. Hukumomi a birnin Ganja sun yi shekaru da dama suna kin yin rajistar kungiyarmu. Saboda haka, ’yan sanda sukan shiga wurin taronmu ba zato, sai su kama kowa da ke wurin kuma sun sa wasu daga cikin ’yan’uwanmu biyan tara. Akwai wani dan’uwa da aka yi ta kama shi da laifi ana ci masa tara, har tarar da aka ci masa ya kai dala 11,375 a lokacin (wajen naira 4,362,767). An ma kulle wasu ’yan’uwa domin sun kasa biyan wannan kudi mai yawa da aka ce sai sun biya.

A 2013 kuma, ’yan’uwa sun shigar da kara mai jigo, Religious Community of Jehovah’s Witnesses v. Azerbaijan, a kotun ECHR domin Azerbaijan ta rage yawan littattafanmu da za a iya shigarwa a kasar.

Ko da yake gwamnati ba ta riga ta yi rajistar kungiyarmu a birnin Ganja ba, abubuwa sun dan gyaru. A shekarun baya-bayan nan, ’yan sanda sun daina takura wa ’yan’uwanmu da suke yin taro a kananan rukunoni a gidajensu. Kari ga haka, ko da yake gwamnati tana bincika littattafanmu kafin a shigar da su, ta yarda a rika shigar da littattafai da ’yan’uwa suke bukata.

Dan’uwa Kiril Stepanov wanda yake tsara ayyukan Sashen Labarai a ofishinmu a Azerbaijan ya ce: “Muna fata wannan gagarumin hukuncin da ECHR ya yanke, zai sa a yi saurin yin rajistar kungiyarmu a Ganja da kuma wasu birane a Azerbaijan. Kuma muna fata cewa a kwana a tashi, gwamnati za ta daina bincika littattafanmu kafin a shigar da su.”

Mun gode wa Jehobah don yadda yake taimaka mana. Nasarar nan da muka samu a kotu ya dada nuna cewa ‘babu kayan yakin da aka kera domin a yaki bayin Allah da zai yi nasara.’​—Ishaya 54:17.