24 GA AGUSTA, 2018
Azerbaijan
Azarbejan ta daure daya daga ’yan’uwanmu domin ya ki saka hannu a aikin soja. Azarbejan
A ranar 6 ga Yuli 2018, kotun lardin Barda a Azarbejan ta kafa wa Dan’uwa Mehdiyeh Emil mai shekaru 18 dokokin da zai rika bi na tsawon shekara daya idan ba ya so a saka shi a kurkuku. Me ya sa? Domin ya ki saka hannu a aikin soja. Kari ga haka, an bashi sharadin cewa ba zai canja adireshinsa ko kuma ya bar Azarbejan ba tare da izinin hukuma ba.
A watan Disamba 2017, Dan’uwa Mehdiyev ya kai kansa District Department of the State Service for Mobilization and Conscription na Barda, wato wurin da ake rubuta sunan wadanda za su yi aikin soja. Ya ki saka hannu a takardar gayyatar shiga aikin soja domin zuciyarsa bai bar shi ya yi aikin soja ba. Da aka tuhume shi, ya bayyana cewa yin hakan ya sabawa imaninsa, sai ya roka a ba shi aikin farin hula a maimakon aikin soja. Amma sun ki, kuma sun ce za a tura wannan batun zuwa ofishin mai gurfanarwa na Lardin Barda.
Bayan da aka yi zama sosai a kan wannan batun, sai kotun Lardin Barda ta same shi da laifi. Ko da yake kotun ba ta yanke wa Emil hukuncin zuwa kurkuku ba, ana ganinsa a matsayin mai laifi domin gwamnatin Azarbejan ba ta riga ta cika alkawarinta na kirkiro aikin farin hula da wadanda ba sa son aikin soja za su iya yi.
Muna farin ciki cewa Dan’uwa Mehdiyev yana riƙe da amincinsa a matsayinsa na dan-ba-ruwansa a cikin wannan mawuyacin hali.—1 Bitrus 2:19.