Koma ka ga abin da ke ciki

19 GA MAYU, 2015
Azerbaijan

Kasar Azabaijani Ta Kara Tsawon Zaman Kurkuku wa Mata Biyu

Kasar Azabaijani Ta Kara Tsawon Zaman Kurkuku wa Mata Biyu

Ma’aikatar Tsaro ta Kasa (MNS) a Azabaijani ta kara wa Shaidun Jehobah biyu wato, Irina Zakharchenko da Valida Jabrayilova, tsawon kwanakin jira a kurkuku kafin a yi musu shari’a. A ranar 17 ga Fabrairu, 2015, MNS ta tuhume su da laifin rarraba littattafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki ba tare da “izini ba” kuma suka tsare su a kurkuku. A ranar 7 ga Mayu, 2015, Kotun Gunduma da ke yankin Sabail ya yarda a tsare su har sai ranar 17 ga Yuli. Kotun ya ki ya yarda a yi musu daurin talala a gida. Wasu lauyoyi da ke wakiltar Shaidun Jehobah sun shigar da kara a kan yadda ake yi wa matan rashin adalci kuma sun nuna damuwarsa a kan yadda hakan yake shafan lafiyarsu. Gwamnati tana kan binciken wasu Shaidun Jehobah.