Koma ka ga abin da ke ciki

15 GA YUNI, 2015
Azerbaijan

Shaidun Jehobah Sun Yi Kira da A Daina Tsare ’Yan’uwansu Ba Bisa Ka’ida Ba a Azerbaijani

Shaidun Jehobah Sun Yi Kira da A Daina Tsare ’Yan’uwansu Ba Bisa Ka’ida Ba a Azerbaijani

A ranar 17 ga Fabrairu, 2015 hukumomi a Azerbaijani sun kama wasu mata biyu Shaidun Jehobah kuma sun tsare su domin suna wa’azi game da imaninsu. An tsare su a inda masu jiran shari’a suke amma ana tsananta musu sosai kamar yadda ake yi wa masu laifi mai tsanani. Ka saurari yadda wani wakilin European Association of Jehovah’s Christian Witnesses ya kwatanta irin yanayin da suke ciki.