Koma ka ga abin da ke ciki

7 GA JANAIRU, 2016
Azerbaijan

Kungiyar Majalisar Dinkin Duniya da ke Kāre Hakkin ’Yan Adam ta ce a saki Irina Zakharchenko da kuma Valida Jabrayilova daga fursuna

Kungiyar Majalisar Dinkin Duniya da ke Kāre Hakkin ’Yan Adam ta ce a saki Irina Zakharchenko da kuma Valida Jabrayilova daga fursuna

Kungiyar Majalisar Dinkin Duniya da ke Kāre Hakkin ’Yan Adam ta ce a saki Irina Zakharchenko da kuma Valida Jabrayilova daga fursuna. An gano cewa ƙasar Azerbaijan ta saka su a fursuna ne don kawai sun zabi addinin da suke so su bi, kuma an ki jininsu ne kawai don addinin da suke bi. Kotun ta ki ba su ’yancin zaban abin da suke so bisa tsarin da ake bi a duniya baki daya. Matakin da Kungiyar Majalisar Dinkin Duniya da ke Kāre Hakkin ’Yan Adam ta dauka ba don an kulle mata biyun nan da aka yi ba ne kawai, amma don a ba su ’yancin bin addininsu.

Kasar Azerbaijan ta ki sakin Irina kamar yadda Kungiyar Majalisar Dinkin Duniya da ke Kāre Hakkin ’Yan Adam ta ce. Ba ta da koshin lafiya shi ya sa ba ta zo kotu ba a ranar 7 ga Janairu, 2016. Shin Alkali Akram Gahramanov zai bi dokar da majalisar ta kafa sa’ad da aka sake soma shari’ar?