Koma ka ga abin da ke ciki

15 GA AFRILU, 2015
Georgia

Shaidun Jehobah Sun Soma Kamfen don Ilimantarwa a Watan Afrilu

Shaidun Jehobah Sun Soma Kamfen don Ilimantarwa a Watan Afrilu

A ranar 1 ga Afrilu, 2015, Shaidun Jehobah sun soma ilimantar da dukan ’yan sanda da wasu ma’aikata a birane da kuma lauyoyi a Jamhuriyar Georgia. Manufar wannan kamfen shi ne a wayar da mutane game da hukunci na musamman da European Court of Human Rights (ECHR) ya yanke a shari’ar Begheluri and Others v. Georgia. Wannan shari’ar game da yadda aka keta ’yancin Shaidun Jehobah ne a Georgia. Kamfen da aka yi ya wayar da kan ’yan doka a kan shari’ar da aka yi da hukuncin da aka yanke da kuma ayyukan ibada na Shaidun Jehobah.

Tarihin Yadda Georgia Ta Goyi Bayan Cin Zali

Daga shekara ta 1999 zuwa 2003 wasu mabiyan wani firist na Orthodox da aka sauke shi daga matsayinsa a Georgia sun tara jama’a don su yi wa Shaidun Jehobah dūka. Ko da yake Shaidun Jehobah sun shigar da kara wajen ’yan sanda sau 784 game da wannan batun da kuma makamantansu, ’yan sandan sun yi kunnen kashi har ma a wasu lokatai sun hada hannu da mutane wajen cin zalin Shaidun Jehobah. Babu karar da Shaidun Jehobah suka shigar da aka dauki mataki a kai. Masu cin zalin nan sun sami karfin gwiwar ci gaba da aikata wannan laifin ne domin hukumomi a Georgia sun ki su dauki mataki a kan kararraki da aka shigar. A wasu lokatai ma suna kai wa Shaidun Jehobah hari a cikin kotu, a tituna da kuma wuraren manyan taronsu.

ECHR Ya Yanke Shari’a

Shaidun Jehobah a Georgia sun shigar da kararraki biyu a kotun ECHR don a daidaita wannan yanayin. Kotun ya yanke hukunci a kan kara ta farko a watan Mayu 2007, a ya kuma yanke hukunci na biyu a kan karar Begheluri and Others v. Georgia a watan Oktoba, 2014. A cikin hukunci biyun da kotun ya yanke, kotun ya ba Jamhuriyar Georgia laifi domin yadda ya goyi bayan cin zalin Shaidun Jehobah, kuma ya bayyana cewa masu cin zalin sun sami karfin gwiwar ci gaba da wannan mummunan halin ne domin Jamhuriyar ta ki ta dauki mataki a kansu. A cikin hukuncin da ya yanke a shari’ar Begheluri and Others v. Georgia, kotun ECHR ya ce, “hukumomi a Georgia sun ba mutane hujjar aikata laifi, kuma hakan ya sa wasu suka kai wa Shaidun Jehobah hari a duk fadin kasar.” b

Abin farin ciki, washegari bayan shari’ar Begheluri and Others v. Georgia, gwamnatin Georgia ta dauki wa’adi a cikin wata sanarwa don ta nuna cewa za ta hana makamancin haka faruwa. Ga wa’adin:

“Georgia ta ba da kai ga kāre ’yancin yin tunani da bin lamiri da kuma addini, da duk dai hakkin ’yan Adam baki daya. Kasar ta kudura ta bi doka a shari’ar kowane dan kasa kuma ta dauki hakkin kāre ’yancin ’yan Adam. Musamman ma ta ce ba za ta kyale wani ya yi abin da ya ga dama ba kuma ba za ta yi shiru ba idan wani ya wulakanta wani.”

Abubuwa Sun Gyaru a Georgia

A yau, yanayin Shaidun Jehobah a Georgia ba daya yake da na shekaru da suka shige ba. Yanzu Shaidun Jehobah suna yin ibadarsu babu tashin hankali kuma ’yan doka suna kāre ’yancinsu. Hakan ya ba Shaidun Jehobah damar gina wuraren ibadarsu kuma a kwanan nan, sun fadada hedkwatarsu a yankin.

Amma wasu ma’aikata ba su san kome game da Shaidun Jehobah ko kuma abubuwan da suka yi imani da su ba, kuma ba su san kome a kan labarin shari’ar Begheluri and Others v. Georgia ko furucin da wannan ma’aikacin gwamnati ya yi ba. Kari ga haka, ’yan addinai suna karfafa wasu su kai wa Shaidun Jehobah hari har wa yau, amma gwamnati ba ta yi kome a kai ba. Alal misali, a shekara ta 2014, Shaidun Jehobah sun shigar da kararraki dabam-dabam na hare-hare guda 30 da aka kai musu. Kari ga haka, Shaidun Jehobah sun shigar da wasu kararraki a kotun ECHR kuma suna jiran hukunci daga kotun. c

Ya kamata wannan kamfen ya taimaka wa ma’aikatan gwamnati su daidaita yadda suke kāre hakkin ’yan Adam a Georgia. Shaidun Jehobah suna godiya cewa gwamnatin Georgia ta dauki wa’adin hukunta duk wanda ya taka doka, kuma suna fatan gwamnatin za ta cika wannan wa’adin ta wajen hukunta wadanda suke wulakanta wasu saboda wariyar addini.

a Members of the Gldani Congregation of Jehovah’s Witnesses and Others v. Georgia, no. 71156/01, a ranar 3 ga Mayu, 2007.

b Begheluri and Others v. Georgia, no. 28490/02, § 145, a ranar 7 ga Oktoba, 2014.

c Tsartsidze v. Georgia, no. 18766/04, an shigar da karar a ranar 26 ga Mayu, 2004 — Mutanen da ’yan doka da kansu suka wulakanta ko kuma wadanda aka wulakanta sa’ad da ’yan doka suna tsaye suna kallo; Biblaia and Others v. Georgia, no. 37276/05, an shigar da karar a ranar 10 ga Satumba, 2005 — Mutanen da ’yan doka da kansu suka wulakanta ko kuma wadanda aka wulakanta su sa’ad da ’yan doka suna tsaye suna kallo; Tsulukidze and Others v. Georgia, no. 14797/11, an shigar da karar a ranar 27 ga Janairu, 2011 — An ki a yi bincike a kan kararraki guda tara da aka shigar a kan yadda aka kai hari domin wariyar addini.