Koma ka ga abin da ke ciki

6 GA AFRILU, 2016
Hungary

Sashen Tunawa da Kisan Yahudawa da ke Kasar Hungary Ya Bude Hoton Dutse don Girmama Shaidun da Hitila Ya Yi wa Kisan Kiyashi

Sashen Tunawa da Kisan Yahudawa da ke Kasar Hungary Ya Bude Hoton Dutse don Girmama Shaidun da Hitila Ya Yi wa Kisan Kiyashi

SASHEN Tunawa da Kisan Yahudawa da ke Budapest babban birnin kasar Hungary sun bude hoton dutse na Shaidun Jehobah guda hudu da aka kashe don su girmama su don tsayin dakan da suka yi duk da hamayyar da suka fuskanta a lokacin Hitila. An yi wannan bikin a ranar 11 ga Disamba, 2015.

Hoton Dutse da ya nuna Shaidun Jehobah guda hudu da Hitila ya yi wa Kisan Kiyashi a lokacin Yakin Duniya na Biyu.

Wadannan maza hudu su ne Lajos Deli da Antal Hönisch da Bertalan Szabό da János Zsondor. Wata gwamnati da ake kira Hungarian Arrow Cross Nazi Party ne ta kashe su a watan Maris ta shekara ta 1945 a biranen Körmend da Sárvár da ke kasar Hungary don sun ki shiga aikin soja a lokacin Yakin Duniya na Biyu. A hoton dutsen, an rubuta sunayensu da kuma kalmomin da ke cikin littafin Ayyukan Manzanni 5:29 da ta ce: “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum.”

Sakatare na harkokin jama’a a Hungary mai suna Dakta Csaba Latorcai yana magana a lokacin bikin.

Sa’ad da sakatare na harkokin jama’a mai suna Dakta Csaba Latorcai yake ba da jawabin budewa ya ce: “Wannan dutsen yana dauke da hoton mazan Shaidun Jehobah guda hudu, ... a matsayinsu na Shaidun Jehobah, sun bi wannan dokar da ta ce ‘kada ku yi kisankai’ kuma suka ki daukan makamai don su kashe ’yan’uwansu da kuma mutane.”

A bikin, manajan Sashen Tunawa da Kisan Yahudawa mai suna Dakta Szabolcs Szita ya ce: “Da dadewa, an manta da Shaidun Jehobah a matsayin wadanda suka sha wahala a hannun Hitila. Saboda haka, an bude wannan hoton don a nuna cewa sun yi nasara. Wadannan maza hudu sun kasance da bangaskiya sosai kuma sun rike aminci har mutuwarsu. Dukansu sun kafa mana misali mai kyau da za mu iya bi a yau.”

Manajan Sashen Tunawa da Kisan Yahudawa mai suna Dakta Szabolcs Szita yana bude hoton dutsen.

Ku tuntubi:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, tel. +1 718 560 5000

Hungary: András Simon, tel. +36 1 401 1118