23 GA OKTOBA, 2019
Japan
Mahaukaciyar Guguwar Hagibis Ta Yi Barna a Jafan
Guguwar Hagibis ta bugi kasar Jafan daga ranar 12 zuwa 13 ga Oktoba, 2019, ta kashe akalla mutane 77 kuma ta jawo ambaliya. Hakan ya jawo rashin wutan lantarki da ruwan famfo a gidaje da yawa. Hukumomi a Jafan sun ci gaba da neman wadanda suka bata. Wannan mahaukaciyar guguwar ce ta fi yin barna sosai a kasar Jafan tun daga shekara ta 1958, kuma ta jawo ruwan sama da ya kai inci 35 a wasu wurare.
Babu wani cikin ’yan’uwanmu da guguwar ta kashe. Duk da haka, mutane goma sun dan ji rauni. Kari ga haka, gidaje fiye da 1,200 na ’yan’uwanmu da kuma Majami’un Mulki guda ashirin da uku sun lalace. Uku daga cikin Majami’un sun lalace yadda ba za a iya yin amfani da su ba saboda suna cike da ruwa da kuma rashin wutar lantarki. Majami’ar Babban Taro da ke birnin Tochigi ya dan lalace.
An kafa Kwamitin ba da Agaji a yankunan Fukushima da Nagano. Za a kafa wasu Kwamitin ba da Agaji bayan ofishin reshe da ke kasar ta gano adadin barna da bala’in ya jawo a wasu wurare. Ana yi wa ’yan’uwa da bala’in ya shafa tanadin abinci da ruwan sha. Masu kula da da’ira a wuraren na karfafa da ta’azantar da wadanda wannan bala’i ya shafa.
Muna da tabbaci cewa Jehobah zai ci gaba da zama mafaka ga ’yan’uwanmu a lokacin da suke fuskantar kalubale mai tsanani.—Zabura 142:5.