Koma ka ga abin da ke ciki

12 GA YULI, 2018
Japan

Ambaliya Ta Yi Barna a Yammacin Japan

Ambaliya Ta Yi Barna a Yammacin Japan

A takaice dai mutane 169 ne suka rasa rayukansu a yammacin Japan, kuma hakan ya hana mutane sama da 255,000 samun ruwa mai kyau cikin gidajensu, bayan wata ambaliya da ta yi barna kuma ta jawo gucewar kasa.

Ko da yake a wannan barnar, ba wani cikin Shaidun Jehobah da ya rasa ransa, amma Shaidu 200 sun bar gidajensu kuma wata ’yar’uwa ta ji rauni. An yi jinyar wannan ’yar’uwar a asibiti kuma tana samun sauki. A kalla barnar ta lalatar da gidajen ’yan’uwa akalla 103, kuma ya hallakar da wani gida gabaki daya. Kuma barnar ambaliyar ta lalatar da Majami’un Mulki 11 da kuma wani wurin Babban Taro.

An kafa kwamiti hudu na tara kayan agaji domin su ta’azantar da kuma karfafa ’yan’uwan da bala’in ya shafe su daga cikin Littafi Mai Tsarki, da kuma taimaka masu da kowane irin taimako da ake bukata, wanda ya kunshi abinci da sutura da kuma ruwan sha. Wannan kwamiti da aka kafa na tara kayan agajin za su yi aiki na tsawon lokaci, wannan aiki zai kunshi share-share da baza maganin kashe kwayoyin cuta da kuma gyara gidajen ’yan’uwan da suka lalace.

Muna addu’a wa ’yan’uwanmu wadanda bala’in ya shafa a kasar Japan yayin da muke begen lokacin da Yesu za ya yi amfani da ikonsa ya cire dukan bala’un da ke cikin duniya har abada.—Matta 8:26, 27.