Koma ka ga abin da ke ciki

24 ga AFRILU, 2017
Japan

Shaidun Jehobah sun taimaka wajen gyaran gidaje 300 da girgizar kasa ta lalata a Japan

Shaidun Jehobah sun taimaka wajen gyaran gidaje 300 da girgizar kasa ta lalata a Japan

Shaidu suna gyara silin da ya lalace a wani gida a Koshi.

EBINA, Japan​—Shaidun Jehobah a Japan sun kammala aikin gyara gidaje 348 da girgizar kasa da aka yi a Kumamato da ke Japan ta lalata a ranar 14 da 16 ga Afrilu 2016. Mutane 15,000 ne suka taimaka a aikin gine-ginen da aka yi tun daga Yuli 2016 zuwa Maris 2017.

Ko da yake babu wani cikin Shaidun Jehobah da ya mutu a sakamakon girgizar kasar, amma ya zama dole wa mutane 119 su bar gidajensu. Da farko dai an sa su a Majami’un Mulki 15, wato wuraren ibadar Shaidun Jehobah. A lokaci wasu ’yan’uwan suna taimaka wa wajen share tarkace a gidajen wadanda bala’in ya shafa.

Rukunin ma’aikatan gine-gine shida suna saka sabon rufi a wani gida da ya lalace a garin Chimachi.

Tun daga ranar 25 ga Yuli, 2016, Shaidun Jehobah masu taimako wajen aikin gine-gine sun yi gyara a wuraren da suka tsage da yin dabe da gyaran bangon ciki da rufi da kuma magudanar ruwa a gidajen da girgizar kasar ta lalata. Sun kuma canja kofofi da windodi da kuma iyakwandishana.

Masu taimako suna gyara wani gida da ya lalace a garin Mashiki.

Mallam Minoru Kono, wanda a dā ma’aikacin tsaro ne a Japan ya lura da wannan aikin da Shaidun Jehobah suka yi, kuma ya ce: “A aiki da nake yi, nuna gaggawa yana da muhimmanci kwarai don cetar da rayuka. Shaidun Jehobah sun nuna irin wannan halin gaggawa bayan girgizar kasa da aka yi a Kumamoto. Don sun hanzarta su taimaki jama’a a inda girgizar ta auku. Ban da haka, a lokacin da Shaidun suka fara aikin agaji na gine-ginen, na yi mamakin ganin cewa ba ‘yan koyo ba ne amma kwararrun magina daga fadin Japan suna zuwa domin su taimaka a aikin. Shaidu masu aikin agajin sun ba da kai sosai kuma sun yi aiki tukuru.”

Masu taimako a aikin gine-gine suna share dattin da aka cire daga rufofin da suka lalace kuma suna sanya sabbobi a Kikuchi.

Wani cikin Shaidun yana kai kankare da za a yi amfani da shi don gyaran tushen wani gida da ya lalace a garin Uki.

Kakakin Shaidun Jehobah mai suna Ichiki Matsunaga ya ce: “A cikin ’yan watanin da suka shige, muna ta aikin gine-gine tare da dubban mutanen da girgizar kasar Kumamoto ta shafa. Taimakon ‘yan’uwanmu bayan wannan bala’i ya sa mun kasance da kwanciyar zuciya da kuzari sosai.”

Inda Aka Samo Labarin:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Japan: Ichiki Matsunaga, +81-46-233-0005