Koma ka ga abin da ke ciki

13 GA SATUMBA, 2018
Japan

Mahaukaciyar Guguwar Jebi ta auku a kasar Jafan

Mahaukaciyar Guguwar Jebi ta auku a kasar Jafan

A ranar Talata, 4 ga Satumba 2018, Arewanci kasar Jafan ta fuskanci matsaloli da yawa saboda da wata Mahaukaciyar Guguwa da aka yi shekaru fiye da ashirin ba a taba ganin irin ta ba. Jami’an tsaro sun ba da umurni cewa a fice daga wuraren da bala’in zai shafa, kuma kamar yadda aka zata, guguwar ta ragargaza wurare.

’Yan’uwan a ofishinmu da ke Japan sun ruwaito cewa babu Mashaidin Jehobah da ya rasa ransa. Duk da haka, akalla ’yan’uwa 15 ne suka ji rauni, kuma guguwar ta lalata da kusan gidaje 538 da kuma Majami’un Mulki guda 44.

Kwamitin Ba da Agaji na Osaka da Sakai sun yi aiki tare don ba da agaji, wanda ya kunshi gyara gidaje da suka lalace da kuma mafi muhimmanci yin ziyarar ban-karfafa ga ’yan’uwa.

Abin farin cikin shi ne, Jehobah yana sane da yanayin da ’yan’uwanmu ke ciki kuma a shirye yake ya yi amfani da kungiyarsa don ya taimaka musu.—Zabura 34:19.