3 GA MAYU, 2017
Kazakhstan
Kasar Kazakhstan Ta Hana Teymur Akhmedov Yin Ayyukan Ibada Kuma An Jefa Shi a Kurkuku
A ranar 2 ga Mayu 2017, wata kotun da ke Astana ta yanke hukuncin jefa Teymur Akhmedov shekara biyar a kurkuku domin yana wa’azi game da addininsa. Shi ne mutum na farko cikin Shaidun Jehobah da ke Kazakhstan da aka hukunta shi tun lokacin da kasar ta sami ‘yancin kai a shekara ta 1991.
An tsare Malam Akhmedov a kurkuku har fiye da wata uku a cewar ana jiran hukuncin da kotu za ta yanke duk da kokarin da kungiyoyin kasashen waje suka yi don a yi masa Daurin talala a gida kafin lokacin da kotu za ta soma shari’ar. Shekarunsa 61 , kuma yana da aure har da ’ya’ya maza uku, kuma ba shi da isasshen lafiya.
An Hukunta Shi Don Ya Yi Amfani da ’Yancinsa na Yin Ibada
A watan Janairu na 2017 ‘yan sandan ciki, wato National Security Committee (KNB) sun kama Malam Akhmedov don suna zarginsa da takā dokar da ke Article 174(2) na kasar Kazakhstan. KNB tana zarginsa da bayyana imaninsa ga wasu a boye kuma hakan zai iya jawo “gāba tsakanin addinai.”
Alkali Talgat Syrlybayev ya yanke hukunci cewa furucin Malam Akhmedov yana jawo “sabani tsakanin addinai” kuma yana “zuga mutane su daina yin tarayya da wasu addinai, da kuma yana ganin kamar sun fi sauran mutane don abin da suka yi imani da shi.” Alkalin ya kuma hana Malam Akhmedov yin “ayyukan ibada” har na tsawon shekara uku.
Lauyan da ke kare Shaidun Jehobah a shari’ar mai suna Philip Brumley ya ce, “Hukumomin kasar ba sa amfani da doka a hanyar da ta dace. A shekara ta 2016, wasu mutane sun gayyaci Teymur zuwa wani gida don ya gaya musu game da imaninsa. Har ma sun ziyarce shi a gida. Teymur bai san da cewa ana daukar muryarsa a tef sa’ad da suke tattaunawa ba, kuma bai san cewa za su yi amfani da wannan bayanin don su tuhume shi a nan gaba ba. Wannan ya nuna yadda hukumomi suke iya kokari don su hana mutane bin addininsu cikin lumana. Kuma hakan tāka doka ne.”
Bugu da kari, iyalin Malam Akhmedov sun damu kwarai don ba shi da lafiya. Yana fama da wani maruru (da ake zato ciwon daji ne), amma hukumomi sun ki su yarda da rokon da aka yi cewa a sauya hukuncin zama a kurkuku da aka yanke ma Malam Akhmedov zuwa daurin talala, kuma ba su yi masa tanadin jinyar da yake bukata ba. Lauyoyinsa sun kai kuka zuwa kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya da ake kira UN Working Group on Arbitrary Detention, da UN Special Rapporteur on freedom of religion and belief, da kuma UN Special Rapporteur on the rights to freedom of peaceful assembly and of association.
Shin, Za a Sami ‘Yancin Gudanar da Ayyukan Ibada a Kasar Kazakhstan?
Shaidun Jehobah sun fuskanci kalubale da yawa a Kazakhstan sa’ad da suke gudanar da ayyukan ibadarsu. Duk da haka, yadda aka jefa Malam Akhmedov a kurkuku sabon abu ne kuma hakan ya ba su mamaki sosai, don ya shafe ibadarsu. Lauyoyin Shaidun Jehobah sun ci gaba da rokon hukumomin kasar Kazakhstan cewa su daraja kiraye-kirayen da kungiyoyi da kuma hukumomin kasashen waje suke yi cewa kada su hana mutane yin ibada.