Koma ka ga abin da ke ciki

17 GA MAYU, 2017
Kazakhstan

Kotun Kazakhstan Ta Jefa Wani Mashaidin Jehobah Marar Lafiya Kurkuku Kuma Ta Hana Shi Yin Ibadarsa

Kotun Kazakhstan Ta Jefa Wani Mashaidin Jehobah Marar Lafiya Kurkuku Kuma Ta Hana Shi Yin Ibadarsa

ALMATY, Kazakhstan​—⁠A ranar 2 ga Mayu, 2017, wani kotu a babban birnin Astana da ke Kazakhstan ta yanke wa Teymur Akhmedov hukuncin shekara biyar a kurkuku don yana ayyukan addininsa. Kotun ta ce yana “jawo sabani tsakanin addinai” kuma yana “nuna cewa addininsa ya fi na wasu muhimmanci.” Ban da jefa shi cikin kurkuku da aka yi, alkalin ya sāke hana Malam Akhmedov daga yin duk wani ayyukan ibadarsa har shekara uku. Malam Akhmedov yana da shekara 61 kuma yana da mata da yara maza uku. Hukuncin da kotun ta yanke ya sa rayuwarsa cikin hadari domin ba shi da cikakken lafiya kuma yana bukatar yin jinya domin wani kumburi da yake da shi, kuma kumburin yana fid da jini, amma kotu ta hana hakan. Malam Akhmedov za ya afil maganar zuwa babban kotu. Za a saurari afil ɗin a watan Mayu ko Yuni.

Wannan shawarar da kotu ta tsai da shi ya tad da na zaune tsaye lokacin da hukuma mai suna National Security Committee ta kama kuma ɗaure Malam Akhmedov bisa dokar Criminal Code of Kazakhstan Article 174(2) na Kazakhstan a ranar 8 ga Janairu. An tsare Malam Akhmedov na watanni da yawa kuma an ki ya nemi jinya. Wani wakilin Shaidun Jehobah da ke hedkwatarsu mai suna David A. Semonian ya ce: “Shaidun Jehobah a duniya gaba daya sun damu sosai game da abin da ke faruwa da Teymur. Muna fatan cewa hukumar za ta sauke zargin da ake yi wa wannan bawan Allahn, kuma ta yarda masa ya kasance da iyalinsa kuma ya yi jinyar da yake bukata.”

Wannan hukuncin da kotun Astana ta yanke ya sa Shaidun Jehobah sun gane cewa Kazakhstan suna bin salon abin da Rasha suka yi musamman ma da Babban Kotun Rasha ta ba da umurni kwanan nan cewa a rufe Ofishin Shaidun Jehobah da ke Rasha. Malam Semonian ya ce: “Kamar yadda aka yi wa addininmu a Rasha, an kama Teymur Akhmedov ne don ana ganin addininmu rukunin ‘yan ta’ada ne, kuma hakan ba gaskiya ba ne. Yanzu dai wasu rukunoni a ƙasar waje, kamar su United Nations Human Rights Committee da kuma United States Commission on International Religious ta gaya wa kotun Kazakhstan cewa su daina amfani da dokar da aka kafa don ‘yan ta’ada suna tsananta wa masu ibadar kirki da shi.” Ya kara cewa: “Muna fatan cewa za a daina tsananta wa dukan ‘yan’uwanmu a Kazakhstan don ayyukan addinin da suke yi da yake taimaka wa mutane a fadin duniya. Muna nan muna sa kunne ga abin da za a yi da wannan al’amarin.”

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Kazakhstan: Bekzat Smagulov, +7-747-671-45-01