Koma ka ga abin da ke ciki

11 GA AFRILU, 2018
Kazakhstan

An Saki Teymur Akhmedov daga Kurkukun Kazakhstan a Ranar 4 ga Afrilu, 2018

An Saki Teymur Akhmedov daga Kurkukun Kazakhstan a Ranar 4 ga Afrilu, 2018

Shugaban kasar Kazakhstan mai suna Nursultan Nazarbayev ya ce a saki Teymur Akhmedov daga kurkuku, kuma an yi hakan a ranar 4 ga Afrilu, 2018. Kafin wannan lokacin, a ranar 27 ga Maris, 2018, hukuma ta yarda dan’uwa Akhmedov ya samu kulawar gaggawa a asibitin da ke birnin Almaty kuma yanzu haka yana samun sauki.

An saka Dan’uwa Akhmedov dan shekara 61 a kurkuku tun ranar 18 ga Janairu, 2017 domin imaninsa. Dan’uwan yana farin cikin don yanzu yana tare da iyalinsa.

Dukanmu muna farin ciki cewa Jehobah ya ceci bawansa mai aminci.—2 Sama’ila 22:2.