Koma ka ga abin da ke ciki

2 GA MARIS, 2015
Kyrgyzstan

Lokacin Daukan Mataki Mai Muhimmanci a Kan ’Yancin Addini a Kyrgyzstan

Lokacin Daukan Mataki Mai Muhimmanci a Kan ’Yancin Addini a Kyrgyzstan

An samu ci gaba a batun ’yancin addini a Kyrgyzstan a ranar 4 ga Satumba, 2014 a lokacin da Constitutional Chamber of the Supreme Court (wato Dakin Tsara Dokokin Kasa na Kotun Koli) ya sanar cewa wasu dokoki a cikin tsarin 2008 Religion Law ba ta cikin tsarin dokokin kasar. Hakan ya ba Shaidun Jehobah ’yancin yin rajistar addininsu a kudancin kasar Kyrgyzstan. a

Duk da sanarwar, hukumar State Committee on Religious Affairs (SCRA) ta ki ta ba Shaidun Jehobah da ke kudancin Kyrgyzstan damar yin rajistar addininsu. Hukumar ta ce ba za ta ba Shaidun Jehobah izinin rajistar addininsu ba sai an yi gyara ga tsarin 2008 Religion Law. Saboda haka, a kudancin Kyrgyzstan an haramta ayyukan ibada na Shaidun Jehobah da aka amince da su a arewancin kasar. b

An Kama Su Saboda Yin Hidimar Ibada Ba Tare da Samun Izini Ba

A ranar 30 ga Yuni, 2014, wata ’yar shekara 46 mai suna Zhyldyz Zhumalieva ta je ta bayyana wa makwabtanta abin da ta yi imani da shi a birnin Naryn a gabas maso kudancin Kyrgyzstan. Hukumomi da ke birnin Naryn suka kama ta kuma suka tuhume ta da laifin bayyana wa makwabtanta addinin da ba a yi rajistarsa ba. c Tun lokacin da Kyrgyzstan ta samu ’yancin kai, wannan ne karo na farko da aka tuhumi wani Mashaidi da laifin yin hidimar ibada.

Bayan da Malama Zhumalieva ta daukaka kara, sai Kotun Gunduma da ke yankin Naryn ya saurare ta a ranar 5 ga Agusta, 2014. Alkalan sun yi tambayoyi da yawa don su kara fahimtar Shaidun Jehobah da kuma wa’azin da suke yi. Bayan sun saurari karar, alkalan sun dakatar da shari’ar har sai lokacin da Dakin Tsara Dokokin Kasa na Kotun Koli ya yanke shawara a kan batun.

Bayan sanarwar sai Kotun Gunduma da ke Naryn ya sake saurarar karar Malama Zhumalieva. Kotun bai same ta da laifi ba kuma ya ce dukan mazaunan kasar suna da ’yancin bin addininsu. Bisa ga shawarar da Dakin Tsara Dokokin Kasa na Kotun Koli ya yanke, kotun ya ce Shaidun Jehobah suna da rajista a kasar Kyrgyzstan. Ya soke hukuncin da kotu na farko ya yanke, amma wanda ya shigar da karar da farko ya daukaka karar kuma ya yi da’awa cewa shawarar da Dakin Tsara Dokokin Kasa na Kotun Koli ya yanke bai shafi karar Malama Zhumalieva ba. Amma, a ranar 24 ga Disamba, 2014, Kotun Koli ya yi banza da karar da ya daukaka. Kari ga haka, ya amince da matakin da Kotun Gunduma da ke Naryn ya dauka na wanke Malama Zhumalieva daga laifi kuma ya daukaka ’yancinta na bayyana wa makwabtanta abin da ta yi imani da shi.

An Yi Adalci Duk da Kullin da Aka Yi a Birnin Osh

A shekara ta 2013, an tsare Oksana Koriakina da mahaifiyarta Nadezhda Sergienko a gida domin ana tuhumarsu da laifin yin wa’azi. Wasu ma’aikata da ke birnin Osh sun kulla wannan sharrin don suna da’awar cewa Shaidun Jehobah suna yin “hidimar ibada da ta saba wa doka.” Ma’aikatan sun ce Shaidun Jehobah ba su da izinin bayyana wa wasu abin da suka yi imani da shi domin ba a yi musu rajista ba.

Kotun da aka fara kai karar a birnin Osh ya wanke matan biyu daga aikata laifi. A ranar 7 ga Oktoba, alkalin da ya yanke shari’ar ya ce ’yan sanda da suka yi binciken karar sun yi kuskure sosai a bincikensu kuma ya ce sun kama Malama Koriakina da Malama Sergienko da laifi domin su Shaidun Jehobah ne.

Wanda ya shigar da karar da farko a birnin Osh ya daukaka kara don a soke shari’ar kotu na farko. Ya ce a mayar da karar don ’yan sanda da suka yi binciken su “gyara” kurakuran da suka yi kuma ya sake shigar da karar Malama Koriakina da Malama Sergienko a karo na biyu. Sa’ad da kotun ya ki amince da abin da mai shigar da karar ya fada, sai dan sandan ya daukaka karar zuwa Kotun Koli na Kyrgyzstan. Kotun ya kafa ranar 3 ga Maris, 2015 don sauraron karar, kuma Shaidun Jehobah suna fata za a sake yanke shari’ar da za ta daukaka adalci.

Shin Gwamnatin Kyrgyzstan Za Ta Daukaka ko Kuma Za Ta Danne ’Yancin Addini?

Wani Mashaidin Jehobah da ya saurari karar Malama Zhumalieva ya ce: “Tun shekara ta 1998, ma’aikata da ke yankinmu suna wulakanta mu domin ba a yi mana rajista a birnin Naryn ba. Yanzu, muna fatan cewa za a yi mana rajista saboda wannan matakin da Kotun Koli ya dauka.”

Shaidun Jehobah suna fata za a yi musu rajista a birnin Naryn da Osh da kuma wasu wurare a kudancin Kyrgyzstan domin hakan zai ba su damar ci gaba da bayyana wa mutane imaninsu ba tare da an tuhume su da aikata laifi ba. Idan Kyrgyzstan ta amince da shari’ar babban kotun da ke kasar, za ta ba mazaunanta ’yancin bin addininsu.

a Ka duba talifin nan “Kyrgyzstan’s Highest Court Upholds Religious Freedom for Jehovah’s Witnesses” don ka ga labarin shari’a da Constitutional Chamber of the Supreme Court (wato, Dakin Tsara Dokokin Kasa na Kotun Koli) ya yanke a ranar 4 ga Satumba, 2014.

b Shaidun Jehobah suna da rajista na kasa da kuma na yanki a arewacin kasar. Amma, hukumomi sun ki su yi musu rajista a kudancin kasar.

c Talifi na 395(2) na Administrative Code of the Kyrgyz Republic ya hana keta “dokokin tsara da yin taron addini da kuma wasu bukukuwa na addini.”