12 GA SATUMBA, 2016
NAGORNO-KARABAKH
An Yi Wa Artur Avanesyan Afuwa Kuma An Sake Shi Daga Kurkuku
A ranar 6 ga Satumba, 2016, hukumomin kasar Nagorno-Karabakh sun saki Artur Avanesyan, wani matashi dan shekara 20, daga kurkukun Shushi bisa ga afuwar da gwamnatin kasar ta yi masa. Malam Avanesyan ya yi watanni 26 a kurkuku bayan kotu ta yanke masa hukuncin watanni 30 a kurkuku don ya ki yin aikin soja. A gaskiya, Artur Avanesyan ya nemi a ba shi wani aiki dabam maimakon aikin soja, amma hukumomin sun yi banza da rokonsa. Matashin ya yi farin cikin sake haduwa da iyalinsa.
Shaidun Jehobah suna murna cewa an saki Malam Avanesyan daga kurkuku. Suna fatan gwamnati za ta amince cewa kowa yana da ‘yancin kin yin wani aiki saboda da imaninsa, kuma ta ba matasan da ke Nagorno-Karabakh damar yin wani aiki dabam, maimakon tilasta su su shiga soja.