Koma ka ga abin da ke ciki

30 GA MARIS, 2017
Peru

Peru: An Ci Gaba da Ambaliya da Tsagewar Kasa

Peru: An Ci Gaba da Ambaliya da Tsagewar Kasa

Yawan ruwan sama ya jawo ambaliya da tsagewar kasa a yankuna kashi 24 cikin 25 a kasar Peru. Kuma rahoto da muka samu ya nuna cewa hakan zai ci gaba da faruwa. An yi ruwan sama sosai fiye da yadda aka saba yi a lokacin damuna wato daga watan Disamba zuwa Maris. Shaidun Jehobah suna taimaka wa ‘yan’uwansu da kuma wasu da ambaliyar ta shafa.

Ambaliyar ta halaka gidaje fiye da 530 na Shaidun Jehobah da kuma wuraren ibada wato Majami’un Mulki guda shida. An ba da rahoto cewa a garin Huarmey da ke da nisan mil 179 daga Lima, babban birnin kasar, ruwan saman ya hana Shaidun Jehobah da yawa da suka hau rufin gidajensu domin ambaliyar, saukowa.

’Yan’uwa da ke ofishin Shaidun Jehobah a Peru sun kafa kwamitocin agaji guda takwas don su kula da Shaidu da ke wuraren da ambaliyar ta shafa. Hakan ya hada da yankuna 12 da gwamnati ta ce suna bukatar taimako da gaggawa. Kwamitocin agajin sun kai ma wadanda ambaliyar ta shafa tan 22 na abinci da kuma ruwan sha fiye da galan 6,000. Za a sake tura tan 48 na abinci da kuma ruwan sha fiye da galan 2,400 a ‘yan makonni nan gaba. Shaidu da yawa a Peru suna taimaka wa da share-share da kuma gine-gine.

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta hanzarta ayyukan ba da kayan agaji daga hedkwatarmu, ta wurin yin amfani da gudummawar da aka ba da don wa’azi a fadin duniya.

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Peru: Norman R. Cripps, +51-1-708-9000