Koma ka ga abin da ke ciki

6 GA MAYU, 2016
Rwanda

An Bi Dokar Kasa a Jamhuriyar Ruwanda

An Bi Dokar Kasa a Jamhuriyar Ruwanda

Shaidun Jehobah sun yi nasara bayan dogon lokacin da suka dauka suna gwagwarmaya a kotu. Muna godiya ga Ofishin Masu Gudanar da Bincike da ke kasar Ruwanda da kuma lauyoyi don kokarin da suka yi wajen ganin mun samu nasara a wannan shari’ar. Da farko, Kotun Koli ya kama Shaidun Jehobah da laifi kuma ya umurce su su biya diyya ga mutanen da hukumomin da ke birnin Kigali suka rushe gidajensu. Amma Ofishin Masu Gudanar da Bincike ya ga cewa hakan rashin adalci ne kuma ya gaya wa Kotun Koli ya yi adalci.

Hukumomin da ke Birnin Kigali Sun Ba da Doka a Tsabtace Mahalli

Don a iya tsabtace mahalli a kasar Ruwanda, hukumomin da ke birnin Kigali sun ba da doka a shekara ta 2006 cewa dukan mutanen da suke da shago a kan hanya su cire su. A wannan dokar kuma an umurci mazaunan garin su rika kiyaye da kuma tsabtace wuraren da suke zama.

Kari ga haka, a wannan dokar an ba da umurni cewa a cire duk gidajen da aka gina ba tare da izinin gwamnati ba kuma hakan ya shafi gidan da Malam Ngayabateranya ya gina a kan hanya. Ya gina gidan ba tare da izinin gwamnati ba kuma ya yi amfani da kayan aiki na gine-gine da bai dace ba da wanda ake amfani da shi a kasar ba. Gwamnati ta ba su kwanaki 21 don su cire irin wadannan gidajen. Amma da kwanakin suka kare kuma ba su yi kome ba, sai magajin garin Gasabo ya rubuta umurnin cewa a rushe gidajen. Da aka rushe gidajen, sai ofishin Shaidun Jehobah da ke Yankin Gasabo, a Remere a birnin Kigali ya kyautata da kuma tsabtace wuraren da ke kusa da su kuma suka sa hanyar wucewa da kuma lambu.

Kotu Ya Kama Shaidun Jehobah da Laifi

Bayan da hukumomin suka rushe gidan Malam Ngayabateranya, sai shi da abokansa suka shigar da kara a kotun Gasabo cewa Shaidun Jehobah ne suka rushe masa gida. Malam Ngayabateranya da kuma abokansa sun ce ya kamata a biya su diyya don gidan da aka rushe amma ba su ba da takamaiman shaida da ta nuna cewa hakan gaskiya ne. Shaidun Jehobah sun ba da takardun da ya nuna cewa hukumomin birnin ne suka yi wannan aikin. Duk da haka, kotun ya ce Shaidun Jehobah suna da laifi.

Babban Kotu Ya Sake Yin Shari’a

Shaidun Jehobah sun daukaka kara a babban kotu don a yi musu adalci. Bayan kotun ya bincika hujjojin, sai ya ce babu wata hujjar da ya sa ya kamata kotun ya kama Shaidun da laifi. A ranar 5 ga Nuwamba, 2010, kotun ya yanke hukunci cewa Malam Ngayabateranya da kuma abokansa su biya diyya don matsalar da suka jawo kuma kudin ya kai dala 1,360.

Kotun Koli Ya Yanke Hukunci ba Tare da Yin La’akari da Takamammun Hujjoji Ba

Malam Ngayabateranya ya daukaka karar ga Kotun Koli na Ruwanda. A lokatan da ake shari’ar babban sakatare na Remera ya ba da shaida cewa Malam Ngayabateranya ya gina gidan ne ba tare da izinin gwamnati ba kuma bisa ga umurnin da Jihar ta bayar na tsabtace mahallin, sai aka rushe gidan. Kotun Koli ta amince cewa ba Shaidun Jehobah ba ne suka rushe gidan. Amma, Kotun ya ce da hadin bakin Shaidun Jehobah ne aka yi hakan. Domin Shaidun Jehobah sun gyara da kuma kyautata wurin bayan da aka rushe gidan, hakan ya sa kotun ya ga cewa da hadi bakinsu ne aka yi hakan. Kotun ya ba wa wadanda suka kai kara kyautar kudin da ya wuce dala 33,000 don barnar da aka yi musu. A ranar 4 ga Afrilu, 2013 ne Shaidun Jehobah suka biya wannan diyya.

Ofishin Masu Gudanar da Bincike ya Dokaci Kotun Koli ya Yi Adalci

Shaidun Jehobah sun kai kara ga Ofishin Masu Gudanar da Bincike domin sharrin da aka yi musu cewa su suka rushe gidan Malam Ngayabateranya. Shugabar Ofishin Masu Gudanar da Bincike a Ruwanda mai suna Malama Aloysie Cyanzayire ta yi bincike a kan karar da kuma hukuncin da Kotun Koli ya yanke.

Bayan Malama Aloysie Cyanzayire ta gama yin binciken, sai ta yi bayani cewa an rushe gidan Malam Ngayabateranya ne domin ya ki ya bi dokar da aka kafa a Ruwanda. Ta gaya wa kotun cewa babu wani kwakkwarar dalilin da ya sa za a daura wa Shaidun laifi don sun bi umurni da aka bayar na tsabtace mahalli. Abin da Shaidun suka yi ya “taimaka wajen kyautata kasar” kuma hakan ya nuna cewa “sun goyi bayan Jihar wajen tsabtace mahallin.”

Gidajen da aka gina ba tare da izinin gwamnati ba kafin a ba da dokar tsabtace mahalli a birnin Kigali da kuma bayan a rushe su

A ranar 4 ga Disamba 2013, Malama Cyanzayire ta ce Kotun Koli ya canja hukunci da ya yanke a kan Shaidun Jehobah. Wasu lauyoyi ne dabam suka yi wannan shari’ar. A ranar 17 ga Oktoba, 2014, Kotun ya kama Malam Ngayabateranya da laifi. Ya dokaci Malam Ngayabateranya ya mayar da kudin da aka ba shi kuma aka ce ya biya diyya. Lauyoyin da suke wakiltan Shaidun Jehobah da kuma ma’aikacin kotun suna aiki yanzu don a mai do da wadannan kudaden.

Dokar Tana Kare ‘Yan Kasar

Shaidun Jehobah suna godiya sosai don taimakon da Malama Cyanzayire ta yi a matsayinta na shugabar Ofishin Masu Gudanar da Bincike da kuma gyarar da Kotun Koli ya yi a batun shari’ar. Babu shakka, dukan ‘yan Ruwanda suna godiya don yadda Jamhuriyar take iya kokarinta wajen ganin an yi adalci da kuma bi doka a kasar.