Koma ka ga abin da ke ciki

7 GA MAYU, 2018
South Korea

Shaidun Jehobah Sun Baza Littattafansu a Wurin Wasan Olymfik na Lafiyayyu da Nakassasu a 2018

Shaidun Jehobah Sun Baza Littattafansu a Wurin Wasan Olymfik na Lafiyayyu da Nakassasu a 2018

A LOKACIN wasan Olymfik na lafiyayyu da nakassasu da aka yi a cikin hunturun 2018 a Pyeongchang wanda ya gudana a 9 zuwa 25 ga Fabrairu, 2018 da 9 zuwa 18 ga Mayu, 2018, ʼyan’uwa maza da mata a Koriya sun fita wa’azi na musamman don raba wa baki littattafanmu kyauta.

’Yan’uwa maza da mata sama da 7,100 ne suka yi wannan wa’azin. Yawancinsu sun zo daga biranen Busan da Gwangju da Incheon da Seoul da kuma Suwon, wasu sun zo ne daga wurare masu nisa kamar tsibirin Jeju a kudancin Pyeongchang wanda sanannen wuri ne na yawon shakatawa da ke da nisan mil 300.

’Yan’uwanmu sun ajiye amalanken wa’azi 152 a wurare 48, har da Gangneung Olympic Park da Pyeongchang Olympic Plaza. Kuma sun samu izinin baza wasu littattafanmu a bakin shiga daya daga cikin cibiyar addinai na Olympic Village.

Amalanken wa’azi guda biyu a kusa da kofar Gangneung Olympic Park.

Haka kuma hukuma ta ba wa ’yan’uwa izinin ajiye amalanken wa’azi a Gangneung Station Square, wanda shi ne tasha na karshe na layin jirgin KTX a yankin Gangneung wanda aka kammala gina shi kwanan nan, da ke jigilan fasinjoji daga Incheon da Seoul da Pyeongchang. A ranar bude wasar, sama da mutane 28,000 ne suka yi amfani da tashan Gangneung.

Domin baki kusan 80,000 su samu littattafanmu a wadace, ’yan’uwa sun ba da takardu da kasidu da mujallu da warkoki a harsuna 20 da suka hada da yaren Caina da Turanci da Kazaktanci da Koriyanci da Rashanci. Hakazalika ’yan’uwa maza da mata da suka kware a yin yaren kurame na Koriya, sun yi amfani da amalanken wa’azi da bidiyoyi domin marabtar kurame da yawa da suka zo Paralympic din. An rarraba littattafanmu fiye da 71,200 har da takardun gayyata zuwa taron Tunawa da Mutuwar Yesu fiye da 22,000.

Shaidun Jehobah a duniya baki daya suna amfani da amalanken wa’azi fiye da 300,000 a kasashe sama da 35. Ta haka ne suke samun damar yin wa’azi ga mutane duk inda suke domin su cim ma hidimarsu.​—2 Timoti 4:5