13 GA YULI, 2018
South Korea
An ’Yantar da Wadanda Suka Ki Yin Aikin Soja Saboda Imaninsu: An Dade Ana Jiran Kotu a Koriya Ta Kudu Ta Yanke Hukunci
Shekaru 65 ke nan ake sa Shaidun Jehobah matasa maza da suka ki shiga soja domin imaninsu a kurkuku. A ranar Alhamis, 28 ga Yuni, 2018, wata Kotu a Koriya ta dau wani gagarumin mataki wanda ya canja tsarin da ake bi a dā. Kotu ta ce dokar da ke Talifi na 5 sakin layi na 1 na Military Service Act ba ta dace ba domin gwamnatin ba ta ba mutane damar yin wani aikin farin hula ba.
Alkalai tara ne suka yi shari’ar, Alkali Lee Jin-sung ne Shugaba, a cikinsu 6 ne suka amince da dokar da za ta ba kowa ’yancin bin imaninsa kamar yadda wasu kasashe ke yi, amma 3 cikinsu ba su amince da hakan ba.
Gwamnatin Koriya ta Kudu ne ta fi saka mutane a kurkuku. A kowace shekara, suna saka mutane a kurkuku don sun ki shiga aikin soja saboda imaninsu. A wani zubin, a kowace shekara akan sa ’yan’uwanmu 500 zuwa 600 a kurkuku. Saka su a kurkuku yana bata musu suna domin bayan an sako su, mutanen yankinsu ba sa daraja su kuma hakan yana sa ya yi musu wuya su sami aiki domin an taba saka su a kurkuku.
Amma kuma, somawa daga shekara ta 2011, wasu ’yan’uwa sun kai kuka wurin hukuma cewa dokar kasar tana tilasta masu su shiga aikin soja ba tare da amincewarsu ba. Shi ya sa tun shekara ta 2012, wasu alkalai sun ga cewa bai dace ba sam a yi wa mutum horo domin ya ki shiga soja saboda imaninsa. Saboda haka, alkalan sun tura karar Shaidun Jehobah zuwa Kotun Tsara Doka don a sake bincika batun.
Aikin Kotun Tsara Doka shi ne ta tabbatar ko doka ta jitu da Dokar kasar Koriya ko a’a. Bayan kotu ta saurari kara sau biyu kuma ta yarda da tsarin dokar shiga soja ta kasar (a 2004 da 2011), yanzu Kotun Tsara Doka ta yarda cewa ana bukatar a yi canji a dokar. Kotun ta umurci gwamnatin Koriya ta Kudu cewa kafin karshen 2019 ta sake tsara wata doka da mutum zai iya yin wani aiki dabam ba dole sai soja ba. Irin ayyukan da za a iya yi su ne kamar aikin asibiti da kuma wasu ayyukan da za su taimaka wa jama’a da ba su kunshi aikin soja ba.
Domin mu gane yadda wannan sabuwar dokar ke da muhimmanci, Dan’uwa Hong Dae-il wanda shi ne kakakin Shaidun Jehobah a Koriya, ya ce: “Kotun Tsara Doka, wanda shi ne mafi karfi wajen kare ’yanci ’yan Adam a kasar, ya ce dole ne gwamnati ta magance wannan matsala. ’Yan’uwanmu a shirye suke su yi duk wani aiki da zai taimaka wa jama’a wanda bai saba wa dokar Allah ba kamar yadda yake a wasu kasashe ke yi.”
Akwai wasu muhimman al’amura da ba a bincika su ba tukuna, wannan ya hada da Shaidun Jehobah 192 da aka sa cikin kurkuku domin sun ki shiga aikin soja da kuma kara 900 da ya kamata a yi shari’arsu.
Da yake Kotun Tsara Doka ta dauki wannan gagarumin mataki, watakila Kotun Koli ba za ta tilasta wa mutane su shiga aikin soja kuma ba. Alkalan Kotun Koli za su tsai da shawara yadda za a yi shari’ar kowane laifi.
Za a saurari shari’ar a Kotun Koli a ranar 30 ga Agusta, 2018, bayan haka kuma za a yanke hukunci. A cikin shekara 14, wannan shi ne lokaci na farko da dukan alkalan Kotun Koli za su zauna domin su yi muhawwara a kan batun wadanda suka ki shiga aikin soja domin imaninsu.
A halin yanzu dai, Majalisar Wakilai ta Koriya tana aiki a kan yadda za a yi gyara a kan dokar Military Service Act wato dokar da ta bukaci kowa ya shiga soja.
Dan’uwa Mark Sanderson memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ya ce: “Muna dokin jin hukuncin da Kotun Koli za ta yanke.” ’Yan’uwanmu a Koriya sun sadaukar da ’yancinsu domin sun sani cewa “wanda ya sha wahala a kan abin da ba laifinsa ba, in ya yi shi saboda yana tunanin nufin Allah ne, abin yabo ne.” (1 Bitrus 2:19) Muna taya su murna domin yanzu kotu ta amince cewa abin da aka yi musu ba daidai ba ne, kuma muna yaba musu domin karfin zuciya da suka kasance da shi a wannan yanayi.