Koma ka ga abin da ke ciki

31 GA JANAIRU, 2017
Thailand

Hukumomin Kasar Thailand Sun Yin Amfani da Littattafan Shaidun Jehobah Don Su Taimaka wa Jama’a

Hukumomin Kasar Thailand Sun Yin Amfani da Littattafan Shaidun Jehobah Don Su Taimaka wa Jama’a

BANGKOK​—Hukumomin Thailand suna amfani da littattafan da Shaidun Jehobah suka wallafa don su koya wa ma’aikatansu darussa dabam-dabam kamar yadda iyaye za su tarbiyyar da yaransu da yadda za a daina yin fada a iyali da kuma yadda za a inganta lafiyar jiki da hankali ko azanci. Wannan watan ne ya cika shekara uku da gwamnatin Thailand take amfani da littattafan Shaidun Jehobah don taimako wajen magance matsalolin jama’a.

Hukumar ilimantarwa ta gwamnatin Thailand ta dauki matakin shirya wuraren koyarwa a yankuna fiye da 8,700 a kasar. Kari ga haka, gwamnatin ta kafa cibiyoyi 11 da ake kira Community Development Learning Centers (CDLC) domin koyar da shugabannin. Wani mai suna Chaiwat Saengsri, wanda ke tsakiyar hoto a gaba, shi ne darektan CDLC a lardin Nakhon Nayok a arewa maso gabashin Bangkok ya ce: “Ayyukan Shaidun Jehobah sun burge ni domin nufinsu a bayyane yake. Suna son jama’a su san Allah mahalicci sosai. Dukanmu abu daya muke so, wato taimaka wa jama’a su zama da mizani domin rayuwarsu ta zama da amintacciyar salama da inganci.” Ya dada cewa: Abin misali shine batun da ke cikin mujalar Awake! Mai talifi ‘How to Avoid Hurtful Speech’ na tare da wani batun da Hukumar zaman lafiya da Tsaron Jama’ a ke koyar wa shugabanni ko kuwa a ce masu angwani. Mun ga amfanin wannan talifin sosai yayin da muke masu koyaswa. Daga baya Malam Chaiwat ya gayyaci Shaidun Jehobah su samar da takardunsu a lokacin da suke taron horarwa tasu ta SMART Leader, inda shugabanni ko kuwa masu angwani 100 da masu horaswa 20 daga lardi dabam-dabam suke haduwa domin karbar horo ta shugabanci da bunkasa zaman jama’a. Cikin hoton nan ta gaba ga Shaidun Jehobah tare da Malam Chaiwat.

Kakakin Shaidun Jehobah a Thailand, Anthony Petratyotin, ya ce: Muna farin ciki da sanin cewa shugabannin jama’a na amfani da littattafanmu na koyar da littafi Mai Tsarki. Za mu ci gaba da samar da littattafanmu wa malaman, tare da ainihin nufinmu​—⁠akin wa’azi.

Inda aka sami Labari:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Thailand: Anthony Petratyotin, +66-2-375-2200