24 GA NUWAMBA, 2020
Turkmenistan
An Saki Dan’uwa Taganov Bayan Ya Yi Shekara Daya a Kurkuku a Turkmenistan
Bayan da aka saki Dan’uwa Selim Taganov daga kurkuku a ranar 3 ga Oktoba, 2020, ya ce: “Na yi addu’a ga Jehobah, kuma ya ba ni kwanciyar hankali.” Shekarun Selim 19 ne yanzu, kuma an kulle shi a kurkuku na tsawon shekara daya domin ya ki shiga aikin soja.
An haifi Selim a birin Ashgabat, wadda ita ce birnin tarayyar kasar Turkmenistan. Sa’ad da yake yaro, yana da ilimi sosai kuma yana son yin waka. Selim yana rubuta wakoki, yana rerawa, kuma ya iya kada jita. Iyayensa da ’yan’uwansa biyu da abokansa sun ce Selim mutumin kirki ne, yana da hankali kuma yana da fara’a. Kafin a kama shi da laifi, lauyan da kotu ta ba wa Selim ya ce: “Shi yaro mai hankali ne, ba ya shan taba, shi ba mai buguwa da giya ba ne, kuma bai dade da kammala karatun sakandare ba. Zama a kurkuku zai bata rayuwarsa ne kawai.”
Rayuwa a kurkuku bai yi wa Selim sauki ba. Amma ya ce: “Zaman da na yi a kurkuku ya sa na kara kusantar Jehobah. A wurin, na tuna abubuwan da na koya daga Littafi Mai Tsarki sa’ad da nake gida, kuma na kara fahimtar su sosai. Na kuma sami karfafa da na tuna nassosi kamar Ishaya 41:10, 11.”
“Da nake kurkukun da ake saka mutane kafin a yi musu shari’a, abin bai yi min sauki ba don babu wanda zan iya gaya masa damuwata. Sai na roki Jehobah ya taimaka min. Bayan haka, wadanda muke kurkukun tare da masu gadi da suka wulakanta ni da farko, sun soma taimaka min, har sun soma karfafa ni. Abubuwan nan sun tabbatar min cewa Jehobah yana tare da ni.”
’Yan’uwa da ke yankin ma sun karfafa Selim. Ya ce: “Da nake kurkuku, ’yan’uwa da dama sun yi ta turo min sakon gaisuwa da kalaman da za su karfafa ni. Na haddace kalaman nan kuma ina ta maimaita su sa’ad da nake ni kadai. Hakan ya karfafa ni sosai.”
Bisa ga dokar kasar Turkmenistan, za a iya sake kiran Selim ya shiga soja. Selim ya san cewa idan hakan ya faru, za a iya kai shi kurkuku na tsawon fiye da shekara daya. Selim ya ce: “Yadda Jehobah ya taimaka min na jimre wannan tsanantawar ya sa ba na jin tsoron duk wani abin da zan fuskanta a nan gaba. Da taimakon Jehobah na zama mai karfin zuciya.”
Dukanmu mun san cewa za mu fuskanci yanayi mai wuya a nan gaba. Selim ya ce: “Ga wadanda za su fuskanci irin wannan jarrabawa, ku tuna abin da Ishaya 30:15 ta ce: ‘Cikin kwanciyar hankali da dogara gare ni za ku sami karfi.’”