14 GA JANAIRU, 2021
Turkmenistan
“Jehobah Ya Taimaka Mini In Iya Jimre Matsalar Nan”
Dan’uwa Eziz Atabayev ya yi shekaru biyu a kurkuku a Turkmenistan domin ya ki ya shiga aikin soja don imaninsa. An sake shi a ranar 19 ga Disamba, 2020. A cikin shekaru goma da suka shige, ’yan’uwa 46 ne aka saka a kurkuku domin imaninsu a kasar.
A shekara ta 2016, gwamnati ta umurci Dan’uwa Atabayev ya shiga aikin soja. Ya ki ya shiga aikin soja saboda imaninsa. An tura kararsa zuwa ofishin mai shigar da kara na birnin. Bayan kusan shekara biyu, sai aka kira Eziz ya bayyana a gaban kotu. A ranar 19 ga Disamba, 2018, kotu ta yanke masa hukuncin yin shekara biyu a kurkuku.
Eziz ya ce: “Kafin a tura ni kurkuku, na tattauna da ’yan’uwa da yawa da aka yi musu shari’a da kuma wadanda aka saka su a kurkuku domin sun ki shiga aikin soja. Na yi hakan ne don in san abin da zan fuskanta a kurkuku. Na karanta labaran ’yan’uwa da yawa a littattafanmu. Na kuma karanta nassosi masu ban karfafa a Littafi Mai Tsarki.”
“Da safe a ranar da za a saurari karata, wani dan’uwa ya karanta mini Ishaya 30:15, ayar ta ce: ‘Cikin kwanciyar hankali da dogara gare ni za ku sami karfi.’ Wannan nassin ya ci gaba da kwantar mini da hankali kuma ya sa na ci gaba da dogara ga Jehobah a duk abin da nake yi. Yin bimbini a kan wannan ayar ya taimaka mini sosai a dukan shekarun da na yi a kurkuku.”
Ko da yake zama a kurkuku ba abu mai sauki ba ne, abin da ya fi damun Eziz shi ne yadda aka raba shi da iyalinsa. Ya ce: “A kurkukun, na kusaci ’yan’uwana da ke wurin. Sun zama abokaina kuma sun sa ba na yawan damu domin yadda aka raba ni da iyalina.”
Eziz ya yi amfani da dukan zarafin da ya samu domin yi wa mutane wa’azi. Ya ce: “Da farko, wasu fursunoni ba su ji dadi domin yadda nake tattaunawa da mutane game da imanina ba. Da shigewar lokaci, wadanda suka ki saurara da farko, sun soma saurara ta. Idan aka kawo sabbin fursunoni kuma na yi kokarin in yi musu wa’azi, sukan ki saurara ta. Amma wadanda na yi musu wa’azi a dā sukan kāre ni kuma su gaya musu abin da suka koya.”
Eziz ya fadi wani abin da zai taimaka mana mu shirya kanmu don jarrabawa da za mu fuskanta a gaba. Ya ce: “Ina karfafa ku ku rika nazari sosai da kuma addu’a ga Jehobah da zuciya daya. Ka gaya masa yadda kake ji da kuma abubuwan da suke ba ka tsoro.”
“Jehobah ya taimaka mini in iya jimre matsalar nan. Ina da tabbaci cewa Jehobah zai sake taimaka mini. Ba na jin tsoron jarrabobi da zan fuskanta a nan gaba.”—Zabura 118:6.