Koma ka ga abin da ke ciki

13 GA JANAIRU, 2021
Turkmenistan

Kotun Soja na Turkmenistan Ta Yanke wa Dan’uwa Ruslan Artykmyradov Hukuncin Yin Shekara Biyu a Kurkuku

Kotun Soja na Turkmenistan Ta Yanke wa Dan’uwa Ruslan Artykmyradov Hukuncin Yin Shekara Biyu a Kurkuku

A ranar 11 ga Janairu, 2021, wata kotun soja a Turkmenistan ta yanke wa Dan’uwa Ruslan Artykmyradov hukuncin yin shekara biyu a kurkuku. Wannan ne karo na biyu da za a saka shi a kurkuku don ya ki shiga aikin soja saboda imaninsa.

Bayan kotun ta sanar da wannan hukuncin, Ruslan ya kasance a natse kuma yana murmushi. Yayin da ake tafiya da shi, ya yi kaulin abin da Yesu ya fada a Matiyu 24:​13, ya ce: “Amma wanda ya jimre har zuwa karshe, zai tsira.”

Bangaskiyar ’yan’uwanmu matasa a Turkmenistan yana karfafa mu. Suna yin koyi da misalin Yesu wanda ya jimre “saboda farin cikin da aka sa a gabansa.”​—Ibraniyawa 12:2.