Koma ka ga abin da ke ciki

Dan’uwa Serdar Dovletov a watan Yuni 2019

9 GA DISAMBA, 2019
Turkmenistan

Kotun Turkmen Ta Yanke wa Dan’uwa Dovletov Hukuncin Shekaru Uku Don Kin Shiga Soja

Kotun Turkmen Ta Yanke wa Dan’uwa Dovletov Hukuncin Shekaru Uku Don Kin Shiga Soja

A ranar 12 ga Nuwamba 2019, wata kotu a Turkmenistan ta yanke wa Dan’uwa Dovletov dan shekara 26 hukuncin yin shekaru uku a kurkuku. Dan’uwa Dovletov yana daya daga cikin ’yan’uwa 10 a kasar da aka saka a kurkuku domin ya kin shiga aikin soja don imaninsa. ’Yan’uwa guda bakwai daga cikinsu an tsare su ne a shekara ta 2019, guda uku kuma a 2018. Za su yi shekaru tsakanin 1 zuwa 4 a kurkuku.

Dan’uwa Dovletov ya fito ne daga birnin Bayramaly na yankin Mary a kudu maso gabashin Turmenistan. Matarsa mai suna Surya da mahaifiyarsa mai suna Sonya Shaidun Jehobah ne.

An fara yi wa Dan’uwa Dovletov shari’a a ranar 11 ga Nuwamba, 2019. Dan’uwa Dovletov ya gaya wa kotun cewa ya ki shiga aikin soja ne domin imaninsa. Kari ga haka, likitoci uku sun yi rantsuwa cewa dan’uwan yana da gyambon ciki mai tsanani da zai hana shi aikin soja.

Duk da kwakkwarar hujja da aka gabatar, alkalin ya ce karya dan’uwa Dovletov ya yi domin ya kauce wa aikin soja kuma ya sa a tsare shi. Ana zato cewa ba da dadewa ba shi ma zai bi sawu sauran ’yan’uwa nan tara da aka tura sansanin Seydi da aka mawuyacin aiki a hamadar Lebap. Dan’uwa Dovletov zai daukaka kara.

Yayin da ’yan’uwanmu a Turkmenistan suke fuskantar rashin adalci, muna yi musu addu’a kuma mun gaskata cewa Jehobah zai taimaka musu su ci gaba da nuna karfin zuciya da kuma aminci.​—Zabura 37:​18, 24.