Koma ka ga abin da ke ciki

Dan’uwa Myrat Orazgeldiyev

7 GA SATUMBA, 2020
Turkmenistan

Wani Kotu a Kasar Turkmenistan Ya Daure Dan’uwa Myrat Orazgeldiyev a Kurkuku don Ya Ki Shiga Soja Saboda Imaninsa

Wani Kotu a Kasar Turkmenistan Ya Daure Dan’uwa Myrat Orazgeldiyev a Kurkuku don Ya Ki Shiga Soja Saboda Imaninsa

Hukunci

A ranar 3 ga Satumba, 2020, Kotun Gundumar Vekilbazar da ke Yankin Mary ya yanke wa Dan’uwa Myrat Orazgeldiyev hukuncin yin shekara daya a kurkuku domin ya ki shiga soja domin imaninsa. Dan’uwan zai daukaka karar.

Karin Bayani

Myrat Orazgeldiyev

  • Shekarar Haihuwa: 2002 (Mary City)

  • Tarihi: Ya yi aiki a wurin sayar da abinci don ya rika samun abin da zai tallafa wa iyalinsu da shi. Mahaifiyarsa ce ta koya masa game da Jehobah. Yana son yin wasanni da rubuta wakoki

Yadda Labarin Ya Soma

Ofishin masu daukan aikin soja sun kira Dan’uwa Orazgeldiyev ya zo ya shiga soja a watan Yuni 2020, wata daya ke nan bayan ya cika shekara 18. Dan’uwa Orazgeldiyev ya bayyana musu abin da ya sa yake kin shiga aikin soja kuma ya ce zai yi aikin farar hula idan aka ba shi.

A ranar 1 ga Yuli, 2020, wakilai guda uku daga ofishin sojoji sun yi kokari su tafi da Dan’uwa Orazgeldiyev. Amma ya ki ya bi su. Jim kadan bayan sun yi kokari su tafi da shi, wani likita ya bincika lafiyar Dan’uwa Orazgeldiyev, kuma sun gano cewa yana da karfin da zai iya yin aikin soja.

A ranar 14 ga Yuli, 2020, masu shigar kara sun kira Dan’uwa Orazgeldiyev zuwa ofishinsu don su yi masa karin tambayoyi. A watan Agusta, an zarge shi da aikata laifi kuma aka saka ranar da za a saurari kararsa.

Muna rokon Jehobah da tabbaci cewa zai amsa addu’armu, zai ci gaba da karfafa Dan’uwa Orazgeldiyev da sauran matasa goma da suke kurkuku, kuma zai ba su karfin zuciya.​—Zabura 31:24.