Koma ka ga abin da ke ciki

Dan’uwa Ruslan Artykmyradov

11 GA JANAIRU, 2021
Turkmenistan

Za A Iya Tsare Dan’uwa Ruslan Artykmyradov a Kurkuku Karo na Biyu

Za A Iya Tsare Dan’uwa Ruslan Artykmyradov a Kurkuku Karo na Biyu

Hukuncin da Za A Yanke

Nan ba da dadewa ba a, wata kotu a kasar Turkmenistan za ta sanar da hukuncin da ta yanke wa Dan’uwa Ruslan Artykmyradov. Za a iya yanke masa hukuncin zaman kurkuku har tsawon shekara biyu don ya ki shiga soja saboda imaninsa. Tun ranar 15 ga Disamba, 2020 ne aka kama shi. Wannan shi ne karo na biyu da ake masa shari’a kuma za a iya kai shi kurkuku don ya ki shiga aikin soja.

Karin Bayani

Ruslan Artykmyradov

  • Shekarar Haihuwa: 2000 (kauyen Alpan Gengeshlik)

  • Tarihi: Ya yi girma a kauye kuma shi makaniki ne. A lokacin da yake makaranta, shi dalibi ne mai ilimi sosai kuma yana son buga kwallo

    Mahaifiyarsa ce ta koya masa yadda zai bi ka’idodin Littafi Mai Tsarki. Yadda Shaidun Jehobah suke nuna kauna da kuma hadin kai ya burge shi sosai kuma hakan ya sa ya yi baftisma a 2015 a lokacin da yake 15. Ya ki shiga aikin soja don yana kaunar Jehobah

Yadda Labarin Ya Soma

A ranar 13 ga Agusta, 2018, an kai Dan’uwa Ruslan Artykmyradov, kurkuku don ya ki yin aikin soja. A lokacin, yana da shekara 18. An sake shi a ranar 12 ga Agusta, 2019 bayan ya yi shekara daya a kurkuku.

Bisa ga dokar kasar Turkmenistan, za a iya kama matasa da laifi sau biyu idan suka ki yin aikin soja saboda imaninsu. Don haka, a watan Nuwamba 2020, an sake kiran Ruslan ya shiga aikin soja.

Ruslan ya sake ki ya shiga aikin soja duk da cewa ya san za a iya sake tura shi kurkuku. A ranar 15 ga Disamba, 2020, an saka shi a kurkuku kuma yana zaman jiran shari’a.

Ruslan ya kuduri niyyar ci gaba da kasancewa da aminci ga Jehobah. Ga abin da ya fada game da shari’a ta farko da aka yi masa: “Ban ji tsoro ba duk da cewa na san za a yi mini shari’a mai tsanani da kuma rashin adalci. Ba zan bar kome ya hana ni farin ciki kuma ya bata dangantakata da Jehobah ba.”

Ruslan ya sha wuya a kurkuku. Yanayin wurin bai da kyau ko kadan kuma sau da yawa akan wulakanta shi. Amma Jehobah ya taimaka masa. Ruslan ya tuna abin da ya faru kuma ya ce: “A lokacin da nake kurkuku, na ga yadda Jehobah ya yi ta taimaka min. Alal misali, na ga yadda Jehobah ya taimaka min a duk lokacin da ake dūkana. Bugu na farko yakan yi mini zafi, amma bayan haka, ba na jin zafin sauran dūkan.” Kari ga haka, yadda ’yan’uwa suka taimake shi ya karfafa shi kuma ya ba da shaida ga mutanen da ke kurkukun.

Ko da yake za a iya saka Ruslan a kurkuku, ya kasance da karfin zuciya kuma ya ce: “Na tabbata cewa Jehobah zai yi min albarka. . . . Idan mutum yana begen wani abu sosai, zai rika farin ciki, idan kuma yana farin ciki, zai sami karfin gwiwa da karfin jimrewa. Mutum mai karfin zuciya ba zai yi sanyin gwiwa ba.”

Misalin Ruslan da sauran matasa masu karfin zuciya kamar shi ya sa mun kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana mu fuskanci kowace jarrabawa da karfin zuciya da kuma farin ciki. Kuma mun san cewa Allah zai sāka musu da alheri don yadda suke saka Mulkinsa farko a rayuwarsu.​—Ibraniyawa 11:6.

a Ba a cika fadin ranar da za a yanke hukuncin a kan lokaci.