Koma ka ga abin da ke ciki

15 GA FABRAIRU, 2016
Turkmenistan

Shekara Daya da Tsare Mutum a Kurkuku Ba Bisa Doka Ba a Kasar Turkmenistan

Shekara Daya da Tsare Mutum a Kurkuku Ba Bisa Doka Ba a Kasar Turkmenistan

A wannan watan Maris ne Bahram Hemdemov zai yi shekara daya a kurkuku tun da hukumomi suka kama shi domin an yi taron addini a gidansa a Turkmenabad, a birnin Turkmenistan. A ranar 14 ga Maris, 2015, ‘yan sanda suka shiga gidansa kuma suka kama shi. Bayan sun yi masa dūkan tsiya sai suka yanke masa hukuncin dauri na shekara hudu, kuma aka kai shi kurkukun Seydi, inda yake aiki kamar bawa.

Dokar kasar Turkmenistan ta yarda mutum ya “bi addinin da yake so ko ya yi ibada tare da wasu,” kuma ta amince da “ ’yancin yin imani da duk abin da mutum ya ga dama da kuma gaya ma wasu abin da ya yi imani da shi.” Amma, har yanzu Bahram yana kurkuku a cikin mawuyacin hali domin ya yi abin da ya jitu da addininsa. Shaidun Jehobah suna roko da ladabi cewa a sake shi.