12 GA DISAMBA, 2019
Ukraine
Kotun Koli na Ukraine ta Kāre ’Yancin Yin Amfani da Majami’ar Mulki
Bayan shekaru hudu na fafatawa a kotu, Shaidun Jehobah a garin Tetiiv, a kasar Ukraine sun sami ’yancin yin ibada a Majami’ar Mulkinsu. Ko da yake ’yan’uwanmu sun gama gina Majami’ar Mulkin tun Disamba 2014, Masu tsara Gine-gine wato State Architect Building Council sun ki ba da izinin yin amfani da ginin har sau shida, kuma suka ci taransu na kudi mai yawa. Kari ga haka, sun soke izinin yin gini da aka bayar duk da cewa an riga an kammala ginin.
A ranar 10 ga Oktoba, 2018, Kotun Koli na Kasar Ukraine ta yanke hukunci cewa ’yan’uwanmu sun bi ka’idodin gine-gine na kasar. Sun nanata cewa Kungiya na Kare Hakkin ’Yan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ta ba kowa ’yancin gina wurin ibada. A ranar 28 ga watan Maris, 2019, wani sabon shugaban Masu tsara Gine-gine a kasar ya ba ’yan’uwanmu izinin da suke bukata. A karshen watan, ’yan’uwa a ikilisiyar sun yi taronsu na farko a wurin.
A ranar 2 ga Nuwamba, 2019, ’yan’uwan sun gayyaci makwabta da jami’an garin, don su zo yawon bude ido a wurin. Wani babba a tsarin yin zane da gine-gine a garin Tetiiv mai suna Anatoliy Fedorovych Zavalniuk, ya ce: “Kun girmama ka’idodin fasahar yin gini, kuma kun bi abin da doka ta tanadar. Wannan wurin ibada ta kara sa wannan sashen birnin da kuma titin kyau sosai. Ina gode muku don wannan aikin.”
Wadannan abubuwa da suka faru, sun ba mu dalilin farin ciki da ’yan’uwanmu a Tetiiv. Muna farin ciki cewa yanzu za su iya yin amfani da Majami’ar Mulkinsu domin su yabi Jehobah su kuma daukaka shi.—Zabura 69:30.