Koma ka ga abin da ke ciki

10 GA YULI, 2015
Ukraine

An Kai Musu Hari Domin Imaninsu a Gabashin Ukraine

An Kai Musu Hari Domin Imaninsu a Gabashin Ukraine

Wasu mutane rike da makamai sun saci Shaidun Jehobah guda 26 tun watan Agusta, 2014, kuma suna wulakanta su don sun tsani addininsu. Shaidun Jehobah da yawa suna zama a wannan yankin kuma an san su sosai da aikin wa’azi da kuma matsayinsu na ba-ruwansu da siyasa. Wasu kungiyoyin azzalumai masu rike da makamai suna amfani da rashin doka da oda da ke yankin su wulakanta Shaidun Jehobah. a

Wulakanci da Wasu Suka Sha

  • A ranar 21 ga Mayu, 2015, ’yan sanda a garin Stakhanov sun kama maza biyu Shaidun Jehobah, masu shekaru sama da 60, domin suna hidimar ibada. Sun tuhume su da “tayar wa mutane da hankali” kuma suka yanke musu hukuncin dauri na kwana 15. A lokacin da Shaidun biyu suke ofishin ’yan sanda, an zarge su da leken asiri kuma suka yi musu tambayoyi game da tsarin kungiyar Shaidun Jehobah. ’Yan’uwa a cikin ikilisiyarsu sun roki lauyan ya saki mutanen amma ya ki. Da farko ba a yarda wa wani danginsu ko kuma ’yan’uwansu masu bi su je wurinsu ba amma daga baya aka bari su kai musu abinci da sutura da magani sau uku a mako. An saki mutum daya daga cikin biyun a ranar 2 ga Yuni, 2015, sa’an nan washegari aka saki dayan kuma aka ba shi oda ya fice daga yankin.

  • A ranar 17 ga Mayu, 2015, wasu mazaje dauke da makamai sun kama Shaidun Jehobah guda hudu suka daure musu idanu kuma suka kai su hedkwatar sojoji a yankin Novoazovsk. Sun yi musu dūkan tsiya na tsawon awa biyu kuma suka yi kamar za su kashe su don su tsorata su. Suka ce wa karamin cikinsu ya shiga soja kuma suka gaya wa dukan Shaidun su furta cewa addinin Orthodox ne kadai addini na gaskiya. Bayan Shaidun sun yi kwana daya a cikin wani matsassen wuri da aka mai da shi kurkuku, sai suka sake su.

  • Irin raunuka da Shaidun Jehobah biyu suka samu sakamakon dūka da aka yi musu bayan an sace su a yankin Novoazovsk

  • A ranar 22 ga Janairu, 2015, mazaje uku dauke da makamai suka saci wani Mashaidi daga wurin aikinsa a Donetsk. Iyalinsa sun kasa sanin inda aka kai shi da kuma dalilin da ya sa aka kama shi. Sa’ad da yake tsare, ya gaya ma wadanda suka kama shi sau da sau cewa babu ruwan shi da siyasa kuma aka sake shi bayan kwana tara.

  • A ranar 9 ga Agusta, 2014, wani dan ta’adda dauke da makami ya saci Shaidun Jehobah guda biyu a Stakhanov, a yankin Luhansk. An tsare su na kwana shida, an yi musu shegen dūka sau da sau kuma an yi kamar za a yayyanke jikinsu ko kuma a karkashe su. Kari ga haka an ki a ba su isashen abinci da ruwa da sutura kuma ba a kula da lafiyar jikinsu ba. Wadanda suka kama su sun matsa musu su musunci imaninsu, su maimaita sharudan Orthodox kuma su yi wa siffofi sujada. Hakan ya nuna cewa wariyar addini ce ta jawo kiyayyar. Duk da wannan wulakancin, Shaidun Jehobah sun ki su musunci imaninsu.

Shaidun Jehobah suna bin imaninsu kuma ba sa yin fada ko kamfen ko ba da kudi don tallafa wa bangarori biyu da suke fada a Ukraine. Sau da yawa mutane dauke da makamai sun kai wa Shaidun Jehobah hari domin halin ba-ruwansu da fada ko siyasa kuma domin ba sa bin addinin Orthodox. Hare-hare da ake kai musu domin su musanta imaninsu ne.

Sun Jimre Duk da Tsanantawa da Ake Yi Musu

Tun da ana jayayya a kan ko waye ke da iko a wannan yankin, Shaidun Jehobah ba za su iya samun taimako daga tsarin dokar yankin ba. Amma sun kai karar wulakanci da ake yi musu zuwa ga kungiyoyin kasashen duniya, har da UN Special Rapporteur on Torture.

Ko da wane irin wulakanci ne za a yi wa Shaidun Jehobah a Ukraine, sun kudura za su ci gaba da nuna halin ba-ruwansu da siyasa da kuma yaki, kuma suna kan yin hidimomin ibadarsu cikin hikima. Suna fata hukumomi da ke yankin za su daukaka ’yancin kowane dan Adam na bin addinin da ya ga dama.

a Mutane dauke da makamai suka kai wa Yuriy hari domin shi Mashaidin Jehobah ne. Shi ne aka nuna hotonsa a farkon talifin. Akwai ranar da aka tare shi a hanya sa’ad da yake dawowa daga hidimar ibada, kuma a wasu lokatai biyu, sun kai masa hari a gidansa. Sun ce masa ya musanta imaninsa kuma ya daina hidimar ibada a matsayin Mashaidin Jehobah.