Koma ka ga abin da ke ciki

31 GA MAYU, 2019
AMIRKA

2019 Takaitawar Taron Yanki na “Kauna Ba Ta Karewa”!

2019 Takaitawar Taron Yanki na “Kauna Ba Ta Karewa”!
  • Kwanan wata: 24-26 ga Mayu, 2019

  • Wuri: Marlins Park a Miami, Florida, Amirka

  • Yaren Taron: Sifanisanci

  • Adadin Mahalarta: 28,562

  • Adadin Masu Baftisma: 230

  • Mutane Daga Wasu Kasashe: 4,600

  • Kasashensu: Ajantina, Bolibiya, Barazil, Burtaniya, Kanada, Amirka ta Tsakiya, Turai ta Tsakiya, Chile, Kolombiya, Cuba, Ecuador, Paraguay, Peru, Filifin, Sifen

 

ʼYan’uwa a kasar suna wa baki maraba a Miami

Wasu Shaidu uku suna daukan hoto a wajen majami’ar taron

Dan’uwa Kenneth Cook, memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu yana yin jawabin kammala taron a ranar Asabar

Ana yi wa mutane hudu baftisma

Ana yin waka da babbar murya a ranar Asabar ta taron

Wata ʼyar Amirka da wata bakuwa suna wa’azi da amalanke a wajen Kislak Center a makarantar Miami Dade College

Masu hidima ta cikakken lokaci baki suna tsaye a majami’ar babban taro sa’ad da ake jawabi na karshe a ranar Lahadi

Wasu ʼyan’uwa mata suna shirye su rarraba abincin da ake kira chorizo, empanadas da paella a wurin da ake marabtar baki

Wasu ʼyan’uwa mata suna rawar ʼyan kasar Sifen a wani bikin da aka yi da yamma

Baki suna jin dadin shirye-shiryen da ake yi a West Palm Beach