Koma ka ga abin da ke ciki

Barnar da guguwar ta yi a Alabama

21 GA JANAIRU, 2020
AMIRKA

Guguwa Ta Yi Ta’adi Sosai a Yammaci da Tsakiyar Amirka

Guguwa Ta Yi Ta’adi Sosai a Yammaci da Tsakiyar Amirka

Dan’uwa Albert Barnett da matarsa Susan Barnett, daga ikilisiyar West Congregation a Tuscaloosa, Alabama

A ranar 11 da 12 ga Janairu, 2020, guguwa mai tsanani ta yi ta’adi sosai a kudanci da yammaci da kuma tsakiyar Amirka. An yi kwana biyu ana ruwa da iska da guguwa, kuma hakan ya yi barna sosai a jihohi da yawa. Abin bakin ciki ne cewa Dan’uwa Albert Barnett da matarsa Susan Barnett, ʼyan shekara 85 da 75 sun rasa rayukansu a cikin gidansu sanaddiyar guguwar.

Ofishinmu da ke Amirka ya ba da rahoto cewa guguwar ta dan bata gidajen ʼyan’uwanmu guda hudu da kuma Majami’un Mulki biyu. Kari ga haka, guguwar ta bata wurin sana’ar wani dan’uwa.

Dattawa da mai kula da da’ira suna taimaka da kuma karfafa wadanda guguwar ta shafa. Mun san cewa Jehobah yana ta’azantar da ʼyan’uwanmu maza da mata wadanda suke makoki don wannan bala’in.​—⁠Zab. 34:⁠18.