Koma ka ga abin da ke ciki

13 GA JANAIRU, 2020
AMIRKA

Karin Bayani: Aikin Agaji Bayan Guguwar Dorian

Jirgin Sama da Na Ruwa Sun Kai Agaji

Karin Bayani: Aikin Agaji Bayan Guguwar Dorian

Mahaukaciyar guguwar Dorian ta yi barna sosai a Bahamas daga ranar 24 ga Agusta zuwa 10 ga Satumba, 2019. Kafin ma a soma guguwar, ofishinmu da ke Amirka ta soma shirya kayan agaji a jihar Florida. Da zarar guguwar ta lafa, sai ʼyan’uwa masu jiragen sama da na ruwa suka shirya kai kayan agaji tsibirin. ʼYan’uwan nan ne mutane na farko da suka kai agaji wurin.

ʼYan’uwa maza da mata 13 sun tuka jirgin sama fiye da sau 300 zuwa tsibirin don su kai kaya mai nauyin kusan kilo dubu dari hudu da kuma masu hidimar ba da kai 700. Kari ga haka, an yi amfani da jiragen ruwa 13 na ʼyan’uwanmu don kai kaya mai nauyin wajen kilo dubu tamanin da biyu. Daga Florida zuwa Bahamas da kuma dawowa tafiyar wajen awa 12 ne.

Manajan tashar jirgin sama na Palm Beach International Airport a Florida, mai suna Jose Cabrera ya ce: “Da zarar ta lafa, jiragen sama na [Shaidun Jehobah] sun ta tashi don su kai kayan agaji Bahamas. Su mutane ne da suke taimakawa sosai.”

Daya cikin ʼyan’uwa da ya tuka jirgin saman mai suna Glenn Sanders, ya ce: “Wannan ne lokaci na farko da yawancinmu muka yi amfani da iyawarmu don mu taimaka wa ʼyan’uwa. Mun yi farin ciki sosai cewa mu karamar gaba ce na jiki da ke taimaka wa gabar da ke shan wahala.”​—1 Korintiyawa 12:26.

Ofishinmu a Amirka ta ce kudin da za a kashe a aikin agajin akalla dala 1,750,000 kuma za a kammala aikin a ranar 1 ga Mayu, 2020.

 

Ana saka kayan agaji cikin jirgin ruwa a Florida, Amirka. ʼYan’uwanmu sun je Bahamas sau 29 a jirgin ruwa

Tashar jirgin sama a Abaco, Bahamas cike da ruwa

Cikin jirgin sama sa’ad da yake tashi