6 GA NUWAMBA, 2020
AMIRKA
Mahaukaciyar Guguwa Mai Suna Zeta Ta Jijjiga Kudu Maso Gabashin Amirka
Inda ya faru
Kudu Maso Gabashin Amirka
Bala’i
A ranar 28 ga Oktoba, 2020, wata mahaukaciyar guguwa mai Mataki na 2 da take tafiya da wuri ta daki Jihar Louisiana. Daga baya karfinta ya ragu kuma ta jawo bala’i a wasu wurare da ke kudancin Amirka
An yi ambaliya a wuraren da ke kusa da bakin teku. Iska mai karfin gaske ta lalata wasu gidaje kuma an dauke wuta a wurare da yawa.
Yadda ya shafi ’yan’uwanmu
Masu shela 324 sun gudu sun bar gidajensu
Mai shela 1 ya dan ji rauni
Abubuwan da aka yi hasararsu
Gidaje 291 da Majami’un Mulki guda 14 sun dan lalace
Gidaje 8 da Majami’ar Mulki guda 3 sun lalace sosai
Gida 1 ya rushe
Agaji
Dattawan da ke yankin, tare da masu kula da da’ira suna kan ziyarar karfafa ga ’yan’uwan da bala’in ya shafa, kuma suna ba da kayan agaji ga wadanda suke bukata. Kwamitin Aikin Agajin da aka sa su kai agaji ga wadanda koronabairas da Guguwar Laura ta shafa ne suke kula da wadanda Guguwar Zeta ta shafa, ba tare da sun karya ka’idodin da aka kafa don cutar koronabairas ba.
Muna bakin ciki cewa wannan guguwar ta jawo wa ’yan’uwanmu matsaloli sosai. Amma Jehobah ya sake nuna wa ’yan’uwan nan kaunarsa marar canjawa ta wajen agajin da suka samu daga ’yan’uwanmu a fadin duniya.—Zabura 89:1.