Koma ka ga abin da ke ciki

19 GA NUWAMBA, 2019
AMIRKA

Wani Ya Kai Hari a Makaranta a Kalifoniya, Amirka

Wani Ya Kai Hari a Makaranta a Kalifoniya, Amirka

A ranar 14 ga Nuwamba, 2019, wani dalibi ya bude wa ʼyan ajinsa wuta a makarantar Santa Clarita, Kalifoniya. Dalibin ya harbi dalibai biyar, biyu sun mutu, uku kuma sun jikata, sa’an nan sai ya kashe kansa.

Muna baki ciki cewa Dominic Blackwell, dan ’yar’uwarmu yana cikin wadanda aka kashe. Shekarunsa 14 ne kuma ba ya fasa zuwa taro da mahaifiyarsa ’Yar’uwa Nancy Blackwell. Dominic ya bar iyayensa da kanne uku. Dattawa suna yin amfani da Littafi Mai Tsarki don su karfafa iyalin da kuma ikilisiyarsu.

Muna bakin ciki sosai da jin wannan abin da ya faru. Muna begen ganin lokacin da Allah zai share “dukan hawaye,” kuma ‘mutuwa, da bakin ciki, da kuka, da azaba’ za su bace.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4.